LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Wani mutumi ya biya N220,000 kudin asibitin mai jegon da aka tsare makonni biyu bayan haihuwa

An tsare Halima da sabon jaririnta a asibiti tsawon makonni biyu sakamakon gaza biyan kudin aikin tiyatan da akayi mata, N220, 000. Bayan rahoton da Vanguard tayi makon da ya gabata, wani mutumin arziki ya biya kudin asibitin kuma an sallameta. 

Vanguard ta samu rahoto daga wata kungiyar kare hakkin yara cewa saurayin Halima ya yi watsi da ita bayan ta samu juna biyu kuma an tsareta a asibiti bayan haihuwa. 

Bayan biyan kudin da mutumin arzikin yayi, manema labarai sun ziyarci sabon jaririn a unguwar Mushin dake jihar Legas inda suke zama. Daga ganin irin muhallin da Halima ke zama, za ka fahimci cewa tana bukatar taimako. 

A cewarta, saurayinta ya ki amincewa da juna biyun da ta samu kuma ya umurceta ta zubar da cikin ko su rabu.  "Na yi iyakan kokarin ganin na zubar da ciki amma abin ya ci tura, amma lokacin da yace inje a zubar min a asibiti ta hanyar tiyata, naki amincewa saboda ina tsoron rasa raina, shi yasa nayanke shawarar ajiye cikin." 

Tace "Na sha bakar wahala lokacin da nike dauke da cikin kuma rokon abinci nike daga wurin mutane. Sau da dama makwabcina, limamin Masallacinmu, ke taimaka min da kudin abinci har zuwa lokacin da na daina iya tambayansa saboda na zaman masa nauyi." "Shine wanda ya bayyanawa mutane labari na saboda in samu taimako." 

"Ina matukar godiya ga mutumin da ya biya kudin asibitina." Halima tana mai kira ga yan Najeriya su taimaka mata a wannan lokaci saboda tana bukatan ciyar da jaririnta da kuma muhalli mai kyau. Ga masu niyyar taimako, Halima na zaune a: No 54, Post Office Road, Muslim, Lagos 


OURCE: LEGIT.NG

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments