--
Wani Likita ya ce burodi da shayi su na iya yi wa mai juna biyu illa a jiki

Wani Likita ya ce burodi da shayi su na iya yi wa mai juna biyu illa a jiki

Shararren likitan nan Dr. Olufunmilayo ya ba masu juna biyu muhimmiyar shawara - Likitan ya bayyana yadda burodi da shayi za su iya yi wa mai ciki da yaronta illa a jiki - A cewarsa, shan shayi zai iya hana jikin mai ciki daukar wasu sinadarai masu amfani Wani likita 

‘dan Najeriya da ke kasar waje, ya bayyana cewa idan mace ta na da ciki, kuma ta na yawan shan shayi ko kuma cin burodi, ta na cikin hadari. Dr Olufunmilayo ya ce shayi da burodi su kan zama illa a jikin mutum ta yadda za su hana shi daukar sinadarin ‘Iron’ 

wanda ya ke taimaka lafiyar ‘dan Adam. Olufunmilayo ya yi wannan jawabi ne a shafinsa na Twiter kamar yadda ya saba fadakar da jama’a. Wannan karo karatunsa ya je ne ga masu iyali ko ma juna biyu. 

Ya na da kyau masu ciki su san abubuwan da ya kamata su rika ci ko sha, da kuma abubuwan da bai kamata su rika yin kusa da su ba yayin da cikin na su ya yi nauyi. 

Mata su kan yi sha’awar ciye-ciye iri-iri a lokacin da su ka dauki juna-biyu, wannan likita ya nuna wasu daga cikin abubuwan da ake ci su na iya taba lafiyar jariri. A cewar likitan, rashin ‘Iron’ a jikin mutum zai iya jawo matsaloli da-dama kamar haihuwar kankanin jariri ko ma ta kai an sauka kafin lokacin haihuwa ya iso. 

Bugu da kari, likitan ya gargadi masu ciki cewa kwankwadar shayi ya na iya yin sanadiyyar da jariri zai fito babu rai, ko kuma ya koma jim kadan bayan an haife shi. Da ya ke karin bayani game da juna-biyu, Olufunmilayo ya ce daukar ciki na jawo karancin jini a jikin mace, 

a dalilin hakane ake nemawa wasu mata sinadarin ‘Iron’. Shayi da bunu kuwa su na jawo karancin wannan sinadari, musamman ace an hada shayin ne da burodi. Likitan ya ce wannan abinci da aka saba ci, mummunan hadi ne.



 Source: Legit.ng 

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Wani Likita ya ce burodi da shayi su na iya yi wa mai juna biyu illa a jiki "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?