LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Uba da Amaryarsa sun kashe diyar uwargida don tayi fitsari a wando

Yan sanda sun samu gawar Autumn Hallow, yar shekara takwas ranar Alhamis bayan kiran gaggawa ta 911 - Kishiyar mahaifiyarta, Sarah Hallow, ta ce ita ma kawai ganinta tayi cikin bayi fuskarta a durkufe. - Bincike ya nuna cewa ta mutu tun kafin zuwan jami'an tsaro Wani mutumi da amaryarsa sun shiga hannun hukuma a birnin Minnesota, 

kasar Amurka bayan kisan diyar uwarigida mai shekaru takwas da haihuwa, Autumn, bayan daureta cikin jakar leda don ta yi fitsari a wando. An tsinci gawan yarinyar cikin randan wanka misalin karfe 3:45 na rana yayinda aka kira jami'an yan sanda, Daily Mail ta ruwaito. 

A cewar ofishin yan sandan Sherburne County, yayinda suka dira wajen sun samu kishiyar mahaifiyar yarinyar, Sarah Hallow, tana kokarin farfado da yarinyar. 

Duk yunkurin da aka yi na ceton rayuwarta ya ci tura yayinda aka sanar da mutuwarta a lokacin. Masu bincike sun bayyana cewa da yiwuwan ta dade da mutuwa kafin a kira yan sanda, 

saboda yanayin yadda aka samu jikinta. Tuni an garkame Uban yarinyar, Brett Hallow da amaryarsa, Sarah Hallow kuma an tuhumesu da laifin kisan kai, a cewar Twin Cities Pioneer Press. 

SOURCE: LEGIT.NG

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments