LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Siyasar Kano: A tsakaninsu dayan ya shunawa dayan EFCC inji Dan Sarauniya

Tsohon kwamishinan ayyuka na jihar Kano Engr. Mu’azu Magaji Dan Sarauniya ya yi gugar zana kan siyasar cikin gida a jam’iyya mai mulki a Kano ta APC.

Dan Sarauniya ya wallafa a shafinsa na Facebook cewar, “An zo wajen sahihin labari daga Abuja ya zo cewa, a tsakaninsu dayan ya shunawa dayan EFCC… an samu karon bukata!”


Wannan na zuwa ne kwana guda, bayan da rahotonni suka tabbatar da cewa hukumar EFCC ta gayyaci kwamishinan kananan hukumomi na Kano Murtala Sule Garo, hakan tasa wannan furuci da Dan Sarauniya yayi ya janyo cece kuce musamman a kafafan sada zumunta.

Tun da farko Dan Sarauniya ya wallafa wasu rubuce-rubuce har karo uku a shafin nasa na Facebook wadanda suka hada da cewar “APC a Kano ai taron kasuwace, akwai APC cinye du, kowa ya santa da mambobinta tsirari, akwai kuma ta maigirma gwamna, APC mai jama’a”.

Haka kuma ya wallafa cewar “Duk sanda ka ji azzalumai sun ce baka da kirki to ka godewa Allah…”.


A watan Afrilun wannan shekara ne gwamnan Kano ya sauke kwamishinan ayyuka na jihar Engr. Mu’azu Magaji Dan Sarauniya bayan wasu kalamai da yayi a shafinsa na Facebook kan shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa marigayi Abba Kyari.

Sai dai daga baya Dan Sarauniya ya musanta tare da neman afuwa.

SOURCE: https://freedomradionig.com/

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments