LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Shigowar 'yan tawayen Al-Qaeda Najeriya: An sanar da 'yan sanda da DSS abinda ya kamata su yi

An umurci hukumomin tsaro da su zauna cikin shiri bayan rahoton da aka samu na cewa muguwar kungiyar Al-Qaeda na shigowa yankin arewa maso yammacin kasar

Kungiyar yaki da ta'addanci ta kuma ja kunnen ‘yan Najeriya da su saka ido tare da gujewa yadda wasu kungiyoyi ke saka farfaganda a harkar tsaron arewacin kasar

Ta ce kamata yayi a hada kai a Najeriya don tallafawa rundunar sojin kasar

An bukaci hukumomin tsaro na fararen kaya da ‘yan sanda sanda da su zauna cikin shiri bayan rahoton da aka samu na cewa muguwar kungiyar Al-Qaeda na shigowa yankin arewa maso yammacin kasar.

Gwamnatin Amurka a cikin kwanakin karshen mako ta ja kunne a kan cewa kungiyar ta’addancin na kokarin mamaye nahiyar Afrika ta hanyar amfani da annobar korona da ta samesu.

A saboda haka ne kungiyar yaki da ta’addanci ta Najeriya ta yi kira ga ‘yan sanda, hukumar jami’an tsaro ta farin kaya da sauran cibiyoyin tsaro da su kasance a cikin shiri.

Kungiyar ta kara da jan kunnen ‘yan Najeriya da su saka ido tare da gujewa yadda wasu kungiyoyi ke saka farfaganda a harkar tsaron arewacin kasar.

A yayin jawabi a madadin kungiyar, Barista Abdulmalik Alfa ya ce kamata yayi a hada kai a Najeriya don tallafawa rundunar sojin kasar.

Kamar yadda Alfa yace, "‘yan sanda, hukumar yaki da fasa kwabrin miyagun kwayoyi, hukumar tsaro ta farin kaya da sauran masu ruwa da tsaki dole ne su taka rawar gani wurin taimakon dakarun sojin.

“Muna son sanar da cewa akwai bukatar masu ruwa da tsaki su saka hannu wurin taimakawa dakarun sojin Najeriya don kawo karshen barazanar Boko Haram da ISWAP a kasar nan.

“Muna son kara jaddada cewa, ‘yan sanda tare da jami’an tsaro na farin kaya da su sake zuba ido a yankunan da aka shafe Boko Haram saboda dakarun sojin tashi suke ba zama ba

“Bayan kwato yankunan da Boko Haram suka addaba, ana tsammanin sauran jami’an tsaro da su koma wurin don sake tsaresu.”

CATN ta yi kira ga dukkan kasashen da ke makwabtaka da Najeriya da su bada tallafin gaggawa don amfanin Najeriya a nahiyar Afrika.


SOURCE: BBCHAUSA

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments