--
Sau biyu kwarto na yi wa mata ta ciki ina kawar da kai - Miji mai neman saki

Sau biyu kwarto na yi wa mata ta ciki ina kawar da kai - Miji mai neman saki

Wani dan kasuwa, Abdullateef Babatunde, ya sanar da kotun gargajiya da ke zamanta a yankin Ile-Tuntun a Ibadan cewa ta raba aurensa da matarsa, Omotayo, saboda ta tilasta ma sa karbar dan da ba nasa ba. Abdullateef ya sanar da kotun hakane yayin da ya ke kare kansa a gaban alkalin kotun, Cif Henry Agabaje, 

bayan matarsa ta yi ikirarin cewa shi mugun mutum ne, a saboda haka a raba aurensu. "Omotayo ta kasance mai cin amanar aure, na sha kamata tana aikata zina da maza daban-daban. "Na kai kararta wurin iyayenta kuma sun bani tabbacin cewa za su yi mata magana domin ta sauya halinta. 

"Amma maimakon ta sauya halinta, Omtayo sai ta kara fandarewa, ta koma karuwanci da gaske, lamarin da ya tilasta min kaurace ma ta tunda ta dauki wata hanya ta daban. "Ta na da yaro tare da daya daga cikin masoyanta. Na taba kamata da kato a shago. "Sau biyu saurayinta ya na dirka ma ta ciki. Mata ta malalaciya ce kuma marar tarbiyya,'' a cewarsa. 

Da take kare kanta, Omotayo; mai sana'ar sayar da abinci, ta bayyana cewa mijinta ba son gaskiya ya ke yi mata ba saboda ya sha bata kudi ta je asibiti domin a zubar da juna biyunsu, yana mai fakewa da cewa bai shirya haihuwa ba. 

"Ya taba gudu ya barni na tsawon shekara biyu da rabi bayan na haifar ma sa yaron farko, sai daga baya ya dawo ya na rokona na yafe ma sa. "Daga baya kuma ya zo ya fara korafin cewa ina sayar da abinci da daddare, shi ba ya so, duk da ba ya iya kulawa da ni da yaron da mu ka haifa," 

a cewarta. Bayan iyayen ma'auratan sun amince da bukatar saki, alkalin kotun ya raba auren domin kowa ya samu zaman lafiya. Alkalin kotun ya umarci matar ta cigaba da rike yaron da su ka haifa yayin da ya umarci Abdullateef ya ke biyanta alawus din N5,000 duk wata domin kulawa da yaron. 


Source: LEGIT.NG


DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657


0 Response to "Sau biyu kwarto na yi wa mata ta ciki ina kawar da kai - Miji mai neman saki "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?