LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Mutuwa ta riski dan fashi yana tsaka da fasadi

Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Edo, ta kashe wani dan fashi da a yayin da yake tsaka da aikata fasadi a wani farmaki da suka kai Benin, babban Birnin jihar.

Daya daga cikin ’yan fashin ya yi gamo da ajalinsa ne a musayar wuta tsakaninsu da jami’an ‘yan sanda a yankin Temboga da ke jihar.

Mai Magana da Yawun rundunar, Chidi Nwanbuzor, ya ce jami’an da ke kula da shiyyar tudun Ikpoba ta cikin birni, sun samu korafi yayin da ’yan fashin ke kwacen dukiyar al’umma a yankin Temboga daura gangaren Ikpoba.

Ya ce da isar jami’ansu wurin da lamarin yake faruwa, sai ’yan fashin suka suka bude musu wuta.

A na tsakar haka ne suka bindige daya daga cikin ’yan fashin yayin da ’yan uwansa suka tsere a wata mota kirar Audi ta wani Mista Daniel Favour kuma daga bisani suka yasar da ita a hanya.

SOURCE: AMINIYA DAILY TRUST

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments