--
Mutane 9 Ne Suka Mutu Bayan Da Wani Kwale-kwalen Ya Kife A Jihar Sokoto

Mutane 9 Ne Suka Mutu Bayan Da Wani Kwale-kwalen Ya Kife A Jihar Sokoto

Mutane 9 ne ake fargabar sun mutu bayan wani kwale-kwalen da suke tafiya da shi ya kife a Birjingo a karamar hukumar Goronyo ta jihar Sokoto. An tattara cewa yawancin wadanda abin ya shafa sun hada da mata da yara, gami da wata amarya da mahaifiyarta.

An tattaro cewa jirgin ruwan yana dauke da fasinjoji 30 a cikin jirgin lokacin da hatsarin ya faru.
An ce fasinjojin suna kan hanyarsu ta zuwa wata gonar shinkafa a hayin kogin inda suke aikin kwadago.

Yayin da yake tabbatar da faruwar lamarin, cansila mai wakiltar gundumar Birjingo, Isa Muhammad, ya ce hatsarin ya faru ne da misalin karfe 8 na safiyar Laraba.
Shugaban kauyen Birjingo, Alhaji Shehu Dangaladima, ya ce jirgin ruwan ya kife ne saboda anyiwa kwale-kwalen yawa.

Mataimakin Shugaban karamar hukumar Goronyo, Zakari Muhammad Shinaka, ya ce; “Nan da nan muka ji labarin hadarin, mun hadar da sama da direbobi 50 wadanda suka yi nasarar kubutar da wasu daga cikin wadanda abin ya rutsa da su.”
A cewarsa, kawo yanzu an gano gawawwaki bakwai yayin da ake ci gaba da binciken sauran gawawwakin biyu.


Shinaka, wanda ya yi ta’aziyya tare da dangin wadanda suka rasa rayukansu, duk da haka, ya umarci Sarakunan Ruwa (sarakunan koguna) a yankin da su hana duk wani jirgin ruwa da yayi lodi fiye da kima da zai tsallake kogunan su.

Ya ce: “Kada a yarda wani jirgin ruwan da aka yi mashi lodi fiye da kima ya ketare kogin naku kuma idan akwai iska mai karfi, bai kamata a kyale jirgin ya motsa ba,” in ji shi.

SOURCE: HUTUDOLE.COM

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN


KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Mutane 9 Ne Suka Mutu Bayan Da Wani Kwale-kwalen Ya Kife A Jihar Sokoto"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?