LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Mayakan Boko Haram sun tare hanya suna yi wa matafiya fashi a kusa a Maiduguri

Ƴan ta'addan kungiyar Boko Haram sun tare titi suna yi wa matafiya fashi a kusa da Maiduguri babban birnin jihar Borno Rahotanni sun ce ƴan ta'addan ba su shiga cikin gari ba kuma ba su harbi kowa ba kawai kuɗi suke karba 

Daga bisani wasu daga cikinsu sun tafi amma wasu sun cigaba da fashin a wajen Maiduguri nisar kilomita 40 daga babban birnin jihar Borno Ƴan ta'addan kungiyar Boko a ranar Talata sun kafa shinge suka kuma rika yi wa matafiya fashi a hanyar Maiduguri zuwa Magumeri kamar yadda Daily Trust ta ruwaito. 

Shugaban mafarauta a jihar, Bunu Bukar, ya ce, "Maharan ba su shiga garin kuma ba su harbi kowa ba; kuma a wajen gari kawai suka tsaya suna tare motoccin da ke shiga da fita. 

"A zuwa yammacin jiya Talata, wasu daga cikin maharan sun tafi amma wasu suna nan, kimanin kilomita 40 daga Maiduguri babban birnin jihar Borno - suna tare motocci suna yi wa fasinjoji fashi."


Source: Legit.ng 

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments