LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Manoman shinkafa 3,383 sun yi batan dabo bayan karban bashin N364m daga CBN

Akalla manoma 3,383 a jihar Taraba sun yi batan dabo da kudin bashi N364m da suka karba daga bankin CBN


Mukaddashin shugaban kungiyar manoman shinkafan Najeriya, shiya jihar Taraba, Tanko Andami ya bayyana hakan

Manoman sun karbi bashin ne tsakanin 2018 da 2019 don noma damina da rani

Kimanin manoma 3,383 da suka karbi bashin N364 million domin noman rani da damina tsakanin 2018 da 2019 a jihar Taraba sun yi batan dabo.

A rahoton The Guardian, reshen kungiyar manoman shinkafa a Najeriya na jihar Taraba (RIFAN), ta bayyana hakan.

Mukaddashin shugaban kungiyar, Tanko Andami, yace kudin da manoman kungiyarsa suka karba bashi sun ki biya, kuma da dama cikinsu sun gudu.

Andami ya bayyana mamakin dalilin da zai sa manoma su ki cika alkawuran da suka dauka ba.

Yace: "Babu ko daya cikinsu yanzu haka da ya dawo da kudin bashin da aka bashi, kuma da dama cikinsu sun gudu."

Babbar bankin Najeriya CBN ta basu bashin ne domin inganta noman shinkafa cikin manufar gwamnatin tarayya na ciyar da kasa shinkafa ba tare an shigo da su daga kasar waje ba.

An baiwa manoma daga kananan hukumomin Lau, Gassol, Wukari, Karim-Lamido, Ardo-Kila da Jalingo karkashin kungiyoyin hadin kai 185.

A cewar mataimakin shugaban kungiyar, Daniel Gani, ya ce yawancin manoman sun yi tunanin kyauta gwamnatin Buhari ta basu.

Ya kara da cewa wasu daga cikin manoman sun canza lambobin wayoyinsu da adireshin da suka bada, har yanzu ba'a samu nasarar samunsu ba.

Ya ce duk da cewa kungiyar na farfadowa ne yanzu, za ta iyakan kokarinta wajen ganin an kwato kudin bashin daga hannunsu.

SOURCE: LEGIT.NG

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments