--
Litar man fetir A Jihar Kano takoma N150 Karanta Dalili

Litar man fetir A Jihar Kano takoma N150 Karanta Dalili

Kungiyar yan kasuwan man fetur masu zaman kansu IMAN, shiyar jihar Kano, ta umurci mambobinta su fara sayar da man fetur a farashin N150 ga lita.

Daily Nigerian ta ce a jawabin da ya saki, shugaban kungiyar na jihar Kano, Bashir Dan-Mallam, ya ce umurnin ya biyo bayan sabon farashin sauyin farashin mai da kamfanin PPMC, mai hakkin sanya farashin mai.

A cewarsa, wannan mataki da suka zamu ya yi daidai da jawabin gwamnati cewa za ta rika canza farashin mai wata-wata dangane da yadda farashin ya canza a kasuwar duniya.

Dan Mallam ya hakaito jawabin PPMC inda ta ce an kara farashin kayan mai zuwa N138.62 ga lita a depot.

Ya ce tuni Depot sun fara sayar musu a farashin N139.5.

Saboda haka, ya umurci dukkan mambobin kungiyar IPMAN dake karkashinsa su fara sayar da litan mai kuma a tabbatar da cewa "kada wanda ya sayar da mai fiye da N150 ga lita."

Legit ta ruwaito muku cewa a ranar Talata, 4 ga watan Agusta, 2020, hukumar PPPRA mai alhakin tsaida farashin kayan mai a Najeriya ta yi karin Naira shida a kan litar man fetur.

PPPRA ta maida kudin litar man fetur N138.62 a manyan tashoshin kasar. Wannan shi ne kudin da za a saida mai kafin ayi jigilarsa zuwa gidaje a watan Agusta.

Dama can kun ji ‘yan kasuwan kasar su na kokarin ganin an maida kudin litar fetur tsakanin N149 zuwa N150 a dalilin wannan canji farashi da aka samu a tashoshi.

A farkon makon nan ne wani ‘dan kasuwa ya shaidawa jaridar Punch cewa kudin fetur zai iya komawa N150 a gidajen mai a wannan watan da aka shiga.

Mataimakin shugaban kungiyar IPMAN ta manyan masu saida mai a kasa, Abubakar Maigandi, ya ce har yanzu PPPRA ba ta sanar da su sabon farashin da aka sa ba.


SOURCE: LEGIT.NG

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN


KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Litar man fetir A Jihar Kano takoma N150 Karanta Dalili "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?