LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Kudin yawon sallah muka fita nema —Yara ‘yan fashi

Wasu samari da aka kama da zargin fashi a hanyar Legas, sun ce sun yi ne domin su tara kudin kashewa a lokacin shagulgulan Sallah Babba.

Yaran su biyar sun tare babban titin Legas daga Ibadan a daidai yankin Ogunmakin a jihar Ogun ana dab da Babbar Sallar.

Aminiya ta zanta da yaran wadanda shekarunsu suka kama daga 15 zuwa 20, a wani kebabben wuri da suke tsare a ofishin rundunar ‘yan sandan SARS da ke Magbon a jihar Ogun.

Wakilin Aminiya ya shaida inda ake tsare da yaran daban ne da wurin da ake tsare da sauran masu laifi. Ba a kulle suke ba kumaba a sanya masu ankwa ba; suna zazzaune ne yayin da wasu jami’an ‘yan sandan ke sa ido a kansu.

—Yadda dubunsu ta cika

Samarin sun shaida wa Aminiya cewa daya daga cikinsu mai shekara 17 ne jagoransu a fashin da suka shirya.

Ya shaida wa wakilinmu cewa sun fita zuwa babbar hanyar ne da misalin karfe daya na dare.

“Mun sa taya a hanya, muka tare hanyar sai mota ta zo muka tsayar da ita, mace da namiji ne a cikin motar.

“Mun ce musu su ba mu kudi, sai suka ba mu. Da matar ta so ta yi gardama sai daya daga cikinmu ya mare ta, da ta ba mu kudin sai ta gudu.

“Mun gama karbar kudi ke nan sai ga ‘yan sanda sun zo da mota sun tsaya daga can baya sun sassauka sun kwanta a kasa, da muka ga haka sai muka gudu muka shiga daji, daga nan muka nufi wajen shanunmu da ke kusa da gida.

“Sai mu biyu muka karasa gida muka bar mutum uku su jira mu a wajen shanu, ko da muka isa gida sai muka ji labarin ‘yan sandan sun kama mutum ukun da muka bari jiran shanu.

“Da gari ya waye sai muka hau mota muka gudu, muka tafi Lokoja a  Jihar Kogi”, inji shi.

— Sun cika rigarsu da iska

 Ya ce kudin da suka karba a wajen mutanen suna da yawa amma bai san adadinsu ba.

Sai dai sun ciri naira dubu ashirin-ashirin su biyu a cikin kudin suka yi kudin mota da su.

Ya ce ba ya zuwa makarantar boko ko islamiyya, ko da yake a baya an kai shi karatun almajirci amma aka dawo da shi gida bayan ya yi rashin lafiya.

— Mun yi ne na wucin gadi

Ya kara da cewa sun fita fishin ne ganin cewa Babbar Sallah ta matso, sai suka yi shawara a tsakaninsu cewa su fita su samo abun da za su rike da Sallah.

“Amma nufinmu idan mun yi wannan fashin ba za mu sake ba. Yanzu ina jin kunya, su abokaina sun ce ni ne babbansu amma gaskiya ba mu da wani babba, kawai muna aiki ne tare”, inji shi.

— Yadda suke yi wa mutane fashi
Daya daga cikinsu mai shekaru 19 ya shaida mana cewa a Jihar Kogi aka haife shi, kafin daga iyayensa su koma Ogunmakin da zama inda suke kiwon shanu.

Ya ce sau uku suna tare hanya da tayoyin mota suna yin fashi da adduna.

“Tsautsayi ne, domin iyayenmu suna ba mu kulawa, suna ba mu abinci.

“Kudin da muka samu a karon farko ba su da yawa, Naira dubu biyar-biyar muka raba, mun ci abinci da su mun kuma sayi katin waya.

“Lokacin da za mu fita na ukun mun yi alkawari ba za mu sake yin fashi ba daga wannan, domin mun fita ne saboda gabatowar Sallah, amma sai ga shi ‘yan sanda sun kama mu”, inji shi.

Aminiya ta kuma zanta da daya daga cikinsu mai kimanin shekaru 19 wanda ya ce shi ya mari matar da suka yi wa fashi.

Ya ce, “A baya ina zuwa makarantar boko a garin Lokoja a jihar Kogi.

“Ina aji biyu na firamare mahaifiyata ta dauko ni ta kai ni Ibadan na yi kiwon shanu saboda mahaifina ya rasu.

“Na fada mata ni karatu nake so amma ta ce kiwo ya fi.

“Wannan fashi da muka yi, mun ga Sallah ta zo ne sai muka ce mu yi sau uku, domin mu samu kudin kashewa da Sallah, sai mu bari saboda Sallah ta iso”, inji shi.

Ya ce ya mari matar ne domin ya ba su tsoro, “Idan ba ka mari wanda kake so ka karbi kudi a hannunsa ka ba shi tsoro ba, to sai ya raina ka ya yi kokarin ya buge ka”.

Sauran yaran da ake zargi su biyu wadanda wakilinmu bai samu jin ta bakinsu ba su ne mafiya karacin shekaru, kuma ba sa jin ko wane yare sai Fulatanci.

— Abin takaici ne ganin yara na aikata manyan laifuka.

Aminiya ta zanta da kakakin ‘yan sandan jihar Ogun, DSP Abimbola Oyeyemi, wanda ya bayyana takaicin ganin yaran masu karancin shekaru suna shiga miyagun ayyuka.

“Fashi babban laifu ne, don haka abun takaici ne a samu yara masu karancin shekaru suna aikatawa.

“Wannan abu ne da za a iya alakanta shi da laifin iyaye; hakkin iyaye ne su kula da tarbiyar ‘ya’yansu”, inji shi.

Ya ce an samu N99,700 cikin N545,000 da suka karba a fashin da suka yi aka kama su.

An kuma same su da wayar salula da suka sace.

Abimbola Oyeyemi ya ce a ranar 17 ga watan Yuli ne ‘yan sanda suka kama wadanda ake zargin su uku a yankin Ogunmakin a jihar Ogun.

Ragowar biyun kuma an kama su ne a garin Okene a Jihar Kogi inda suka gudu domin neman mafaka.

SOURCE: https://aminiya.dailytrust.com.ng/

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments