LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Kamen mabarata a Kaduna ya janyo ce-ce ku-ce

Rashin jituwa ta kaure tsakanin gwamnatin jihar Kaduna da kungiyoyin masu bukata ta musamman saboda fara kamen mabarata.

Cikin mutanen da aka kama sun hadar da makafi, da guragu, da kurame mata da tsofaffi.

Wasu daga cikinsu sun shaida wa BBC cewa jami'an tsaro sun cafke su ne ranar Juma'a, a babban birnin jihar, lokacin da suke bara a kan tituna.

''An kama mutane da yawa, wasu a Kawo, wasu a Unguwar Sarki, wasu a Kano Road'' In ji wani mabaraci da muka zanta da shi.

Wasu daga cikinsu sun yi korafi a kan munin yanayin wurin da aka ajiye su, ga shi babu abinci babu ruwan sha kamar yadda mutumin wanda ya buƙaci a sakaya sunansa ya bayyana.

''Wani wuri ne ma, akwai kashin awaki, nan muke fitsari, ga sauro, ba abinci, kuma tun da aka kama mu babu wanda ya kawo mana abinci, sai dai wadanda suke da kudi in masu abinci sun kawo su saya''

To sai dai gwamnatin jihar a ta bakin Hafsat Muhammad Baba, kwamishiniyar kula da walwalar jama'a ta ce daukar wannan mataki ya zama dole ganin yadda mabaratan ke saba dokokin da aka gindaya, da kuma rashin bin ka'idojin gwamnati.

Ta kuma ce wasu al'umomin da ke zaune a wuraren da suke bara ne suka gabatar da ƙorafi a kan yadda almajiran suke ɓata muhalli.

Me kungiyoyin mabaratan ke cewa ?

Su dai masu bukata ta musamman na nuna fushinsu a kan matakin gwamnatin jihar, da suke ganin ya saba da alkawarin da ta yi musu lokacin da a ke yakin neman zabe.

Sakataren yada labarai na kungiyar masu bukata ta musamman ta jihar Kaduna Kwamared Muntari Saleh, ya shaidawa BBC cewa sun zauna da gwamnatin a baya, har ma a ka musu alkawarin cewa ba za a kama kowa ba har sai an sama musu abin yi.

''Kwatsam sai aka wayi gari a na bi lungu da sako, ko kai mabaraci ne ko kai ba mabaraci ba ne, idan aka ga kai mai nakasa ne, za a yi caraf a kama ka, an kama mana sama da mutum dari an je an kulle yanzu haka''.


Ya jaddada damuwarsu a kan yadda gwamnatin jihar ta jibge mutanen da aka kama wuri guda ba tare da nuna ko in kula game da halin da a ke ciki na cutar korona ba, abinda gwamnatin ta musanta.

Matsalar bara a arewa

Matsalar bara dai matsala ce da ta yiwa yankin arewacin Najeriya katutu, sau da yawa a kan danganta ta da masu bukata ta musamman ko yaran da ake aikawa almajirci daga bisani su bige da neman abinci, sai dai a kashin gaskiya akwai tarin mutanen da rashin abin na kai ke sa su shiga harkar duk da suna gida tare da iyalansu.

Shi yasa wasu ke danganta lamarin da talauci, a ke kuma yin kira ga gwamnati ta tashi tsaye wajen samawa jama'a aikin yi, ko kuma inganta yanayin nema a kasar ta yadda jama'a za su tashi tsaye don neman na kansu.

Jihohin Arewa da dama sun sha yin yunkurin hana bara, don ko da a wannan lokaci na annobar korona gwamnonin jihohin sun amince kowacce jihar ta kwashe almajiranta, sai dai a zahiri har yanzu mabarata na cigaba da cin kasuwarsu.


Yayin da har yanzu ake cigaba da muhawara game da dacewa, ko rashin dacewar gwamnati ta kyale marasa karfi su yi bara, masharhanta na kara jaddada cewa akwai banbanci sosai tsakanin bara, da kuma almajirci, wanda ke nufin neman ilimi.

SOURCE: BBCHAUSA

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments