LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Hotuna: Katin gayyatar ɗaurin auren Hanan Buhari da Turad Sha'aban ya fito

Katin auren 'yar autan Shugaba Muhammadu Buhari, Hanan da Turad Sha’aban ya fito. Za a daura auren ne a ranar Juma'a 4 ga watan Satumbar shekarar 2020 misalin karfe 2 na rana. Ana sa ran za a daura auren ne a fadar shugaban kasa ta Aso Rock Villa da ke babban birnin tarayya Abuja.


Wannan shine daurin aure na farko da za a daura a fadar shugaban kasar ta Aso Rock. Angon dan tsohon dan majalisa ne, Alhaji Mahmud Sani Sha'aban da ya wakilci mazabar Zaria a Majalisar Wakilai ta Tarayya daga Mayun 2003 zuwa Mayun 2007.

Sha'aban kuma tsohon dan takarar gwamna ne a jihar Kaduna a karkashin tsohuwar jami'yyar Action Congress of Nigeria wato ACN. Kazalika, Alhaji Mahmud Sani Sha'aban ne wakilin Tudun Wadan Zazzau. R

Ba za ayi taro irin yadda aka saba ba na bikin aure duba da cewa har yanzu akwai annobar korona a kasar a cewar katin gayyatar hakan na nufin ba mutane da yawa za su hallarci daurin auren ba. Ga dai katin gayyatan auren nan a kasa kamar yadda shafin Linda Ikeji ya ruwaito.

An fitar da katin gayyatar daurin auren Hanan Buhari da Turad Sha’aban. Hoto daga LIB Source: Twitter

SOURCE: LEGITNG

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments