--
 Hotuna: Hankalin jama'a ya tashi sakamakon rushe kasuwar Panteka da za a yi a Kaduna R

Hotuna: Hankalin jama'a ya tashi sakamakon rushe kasuwar Panteka da za a yi a Kaduna R


Acigaban rade-radin shirin rushe tsohuwar kasuwar Panteka da ke kan titin Enugu a kusa da Polytechni ta jihar Kaduna, ya ci gaba da tsorata 'yan kasuwar da duk wasu masu samun abin masarufi daga kasuwar. 


Wannan rade-radin ya tada hankalin makera da sauran masu siye da siyarwa da ke wurin. Tsoronsu ya sake yawaita tun bayan da aka rushe fitacciyar Kasuwar Barci wacce take da kusancin kilomita kalilan daga su. 

Kasuwar ta yi shekaru birjik da kafuwa kuma ta samo sunanta ne daga wata mata mai suna Panteka, wacce ke hada tukwanen karfe tana siyarwa a tsohon sashin kassuwar da ake kira da 'Yantinka. Tare da sauran makeran da ke kasuwar 

da kuma Panteka, yawansu ya ci gaba da hauhawa a cikin shekaru kalilan. Ko bayan mutuwarta, wurin ya ci gaba da zama babbar kasuwar karafa da kayan gini a Najeriya. 

A matsayinta na babbar kasuwar karafuna a Najeriya wacce ta kware a kere-kere, tsohuwar kasuwar Panteka na da sassa 40. 



Kowanne sashi na da abu daya da makeran yankin suka kware a kerawa. Kasuwar ta kasance babban wurin horar da dalibain Polytechnic ta jihar Kaduna tare da sauran manyan makarantu a fadin arewacin Najeriya. 

Cike da tsoron rushe kasuwar, shugaban makarantar, Farfesa Idris Bugaji, ya yi kira ga gwamnatin jihar da ta sake duba wannan hukuncin nata. A maimakon rushe kasuwar, ta mayar da ita wani wurin tarihi sakamakon tsohon tarihin da kasuwar ke da shi a yankin arewacin Najeriya. 

Farfesa Bugaje ya ce, "Ina so in yi amfani da wannan damar wurin kira ga Gwamna Nasir El-Rufai da ya mayar da Kasuwar Pantkea ta zama wurin tarihi. Kada a rusheta, a mayar da ita wurin tarihi a jihar."

Shugaban makarantar ya kara da cewa, "Idan ana son yin sabon gini, a bar tsohuwar Kasuwar Pantekan. Zai yi kyau idan aka gyara kasuwar tare da inganta ta sannan aka mayar da ita wurin tarihi."

 Ya tabbatar da cewa, rushe kasuwar zai durkusar da makera da masu saide-saide a kasuwar tare da jefa makarantar da ke da makwabtaka da ita cikin wani mawuyacin hali. 


Source: Legit.ng


DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to " Hotuna: Hankalin jama'a ya tashi sakamakon rushe kasuwar Panteka da za a yi a Kaduna R"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?