--
Ganduje ya kwace kwangilar gyaran hanya

Ganduje ya kwace kwangilar gyaran hanya

Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya soke ayyukan gyaran titin  Dawakin Tofa, da aka bayar tun shekaru takwas da suka wuce.


Bayan soke kwangilar daga kamfanin Rocad Construction Nigeria Limited , gwamnan ya bayar da aikin ga kamfanin CCECC na kasar China a kan Naira miliyan 651.9.


“Majalisar zartarwata kuma amince da sauye-sauye da kuma karin da aka samu a kudin aikin gyaran Gadar Bagauda a hanyar Wak-Tiga a Karamar Hukumar Bebeji”, inji Kwamishinan Watsa Labarai Muhammad Garba.


A shekarar 2012 jihar ta ba wa kamfanin Rocad aikin mayar da titin Dawakin Tofa mai hannu biyu, amma kamfanin ya yi watsi da shi tare da jefa ‘yan yankin cikin wahala.


Muhammad Garba, ya ce jihar ta kafa kwamitin duba yanayin tafiyar sauran ayyukan tituna masu hannu biyu a fadin jihar domin aunawa da sake tsari da kammalawa a kan kari ko kuma soke ayyukan titunan.


SOURCE: AMINIYA DAILY TRUST

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657


0 Response to "Ganduje ya kwace kwangilar gyaran hanya"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?