--
Fyade: Kauyen Abuja da 'yan mata ba sa zuwa makaranta don tsoron fyade

Fyade: Kauyen Abuja da 'yan mata ba sa zuwa makaranta don tsoron fyade

Burin Hadiza mai shekara 20 shi ne ta zama 'yar jarida mai karanta labarai, sai da ta kasa cimma wannan buri saboda fyaɗen da wasu zauna-gari-banza suka yi mata a hanyarta ta zuwa makaranta.

Hadiza na da shekara 18 aka yi mata fyaɗe, lokacin tana shirin rubuta jarrabawarta ta ƙarshe a sakandare.

"Ina tare da kawayena muna hanyar zuwa makaranta sai suka auko mana, sai kawayena suka gudu suka bar ni, har suka zo suka kama ni suka yi mani fyaɗe.

"Na yi ihu sosai amma babu wanda ya kawo mini ɗauki saboda ba a cika bin hanyar ba," in ji ta.

Hadiza (ba shi ne sunanta na gaskiya ba). tana zaune ne a ƙauyen Zhiko da ke Bwari a Abuja babban birnin Najeriya.


Zhiko ƙauyen ƙayau ne wanda babu wasu ababen more rayuwa na a zo a gani, kuma babu makarantar sakandire kwata-kwata.

Hadiza na tafiyar kilomita da dama kafin ta je makarantarsu da ke Bwari wadda ake kira New Bwari Secondary School.

Daga makarantar zuwa ƙauyensu Hadiza, tafiyar kusan kilomita 10 ne, tana shafe sa'o'i huɗu a tafiyarta da kuma dawowarta makaranta.

Ba ta farin ciki idan tana wannan doguwar tafiyar, kuma tana tafiya makaranta ne tun 5:00 na asuba.

Domin ganin cewa ta je makaranta kan lokaci kuma ta kauce wa ramukan kan hanya da kuma tsallake rafi, tana bin wata ƙaramar hanya da ta ratsa cikin gonaki, kuma ba tsaro a wurin.

A lokacin damina, ciyawar da ke ƙauyen na yin tsayi har su kere tsawon Hadiza.

Bayan ga abokanta da a wani lokaci suke tafiya makaranta a tare, ta kuma saba da kukan tsuntsaye da kuma raɓa da sassafe.





Ta bayyana cewa hanyar da take bi mai kaɗaici na saka ta tana tunani da kyau, amma cikin irin waɗannan ciyayin, akwai masu fyaɗe ɓoye da ke harin yara 'yan makaranta.

A irin wannan hanyar ce aka yi wa Hadiza fyaɗe kuma aka yi mata ciki.

"Ina jin kunya domin bai kai shekarun da za a ce na haihu ba.

"Lokacin da na ke naƙuda, na kasa haihuwa wanda hakan ya ja aka yi mani aiki," ta shaida mana haka cikin rashin jin daɗi.

Sakamakon tana da ɗa namiji, tana sayar da itace kuma tana zuwa gona.

Irin abin da ya faru da Hadiza bai da bambanci da abin da ya faru da wasu matan a ƙauyen.

Akwai wata mai suna Mercy da zauna gari banza suka yi wa fyaɗe wanda ita ma suka kashe mata burinta na zuwa makaranta.

Ta samu ciki har ta haifi 'yan biyu wanda daga baya ta zo ta yi aure a wani ƙauye.

Irin wannan lamari na kashe gwiwowin mata da dama da ke da burin zuwa makaranta domin gina rayuwa mai amfani a garesu.

Happiness Yohana ta sha da ƙyar, bayan ta gudu yayin da masu fyaɗe suka biyo ta a hanyarta ta zuwa wata makarantar sakandire da ke Sabon Wuse a jihar Neja.

Tun daga lokacin ta daina zuwa makaranta, sai dai daga baya iyayenta suka ɗauke ta inda suka kai ta wurin gwaggonta domin ta kammala karatu.

"Akasari sakamakon tafiya mai tsawo da muke yi, muna gajiya ƙwarai a cikin a ji kuma ba mu fahimtar karatu."

Iyaye na kukan a kawo musu ɗauki
Linda Danjuma wadda ita ce shugabar mata a ƙauyen ta bayyana cewa in dai 'ya'yansu mata ba su zuwa makaranta, ba za su samu rayuwa mai amfani ba.

Ta roƙi gwamnati da ta kawo musu makarantar sakandire.

Ta bayyana cewa akasari lokacin da yaransu mata ke zuwa makaranta suna cikin ruɗu

Ta kuma bayyana cewa sakamakon wahalar da suke sha na tafiya makaranta da dawowa, da dama daga cikinsu suna gajiya kuma ba su iya yin aikin gida da makaranta ke ba su.

Philip Yohanna ya ce abin na yi musu zafi ganin cewa suna shan wahala su je gona domin tabbatar da cewa yaransu sun je makaranta, sai dai daga baya kawai su ga an yi musu ciki.

Ya ce wasu iyayen yaran da ke da kuɗi, sun siya wa 'ya'yan su abin hawa domin su je makaranta, waɗanda ba su da hali kuma babu yadda za su yi.

Ya bayyana cewa sun kai ƙarar irin wannan lamari zuwa hukumomi, amma babu abin da ya sauya.

Mai magana da yawun 'yan sandan Abuja babban birnin ƙasar ya ce 'yan sandan na aiki kafaɗa da kafaɗa da al'ummar domin daƙile wannan matsala.

Sai dai ma'aikatar ilimi ta birnin tarayyar da kuma ƙaramar hukumar Bwari, sun bukaci 'yan ƙauyen su samar da kadadar fili biyu domin ginin makaranta, amma har yanzu ba a yi komai ba.


SOURCE: BBCHAUSA

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Fyade: Kauyen Abuja da 'yan mata ba sa zuwa makaranta don tsoron fyade"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?