--
Duba Dalili biyar da ya sa rikicin Kudancin Kaduna ya-ƙi-ci-ya-ƙi-cinyewa

Duba Dalili biyar da ya sa rikicin Kudancin Kaduna ya-ƙi-ci-ya-ƙi-cinyewa

Kaduna, na ɗaya daga cikin jihoihin Najeriya mafi fama da matsalolin tsaro kamar hare-haren 'yan fashin daji a yankin Birnin Gwari da kuma rikicin ƙabilanci musamman a yankin Kudanci.

Gwamnan jihar Nasir Elrufa'i ya ce rikicin Kudancin Kaduna ya samo asali ne tun cikin 1980, lokacin da wasu suka far wa mutane a Kasuwar Magani tare da hallaka mutum 11.

Ya ce rikicin ya ƙara rincaɓewa kuma a 1992 inda aka kashe kimanin mutum 1,300 a Zangon Kataf kan wata rigima game da kasuwa.

Kimanin shekara 40 ke nan ake ta fama da wannan rikici na Kudancin Kaduna, sai dai ga alama lamarin ya faskara, duk da ƙoƙarin da hukumomin ƙasar ke cewa suna yi don kwantar da wutar rikicin.

Ko a baya-bayan nan, rahotanni sun cewa an kashe gomman mutane a rikicin ta hanyar kai hare-hare masu kama da na sari-ka-noƙe a yankin.

To ko waɗanne dalilai ne suka sa rikici ya ƙi lafawa duk da ɗumbin jami'an tsaron da hukumomi ke cewa sun tura don shawo kan al'amura da kuma kwantar da wutar rikici?

Yayin zantawarsa da BBC a baya-bayan nan, Gwamnan Kaduna, Nasir Elrufa'i ya zayyana wasu dalilai. Ga su kuma kamar yadda muka tsakuro muku:

Wannan layi ne
Amfani da siyasa da addini da ƙabilanci

Gwamna Elrufa'i ya zargi wasu abokan hamayyar siyasa da ya ce an kayar da su zaɓe amma ba su yarda da karɓar ƙaddara ba, don haka suke neman hanyar tayar da hankali.

Ya kuma ce irin waɗannan 'yan adawa: "sun rantse, sai sun tabbatar jihar nan (Kaduna) sai an kasa mulkinta.

Matsalar baƙi da ɗan gari

Nasir Elrufa'i ya kuma ce akwai wasu mutane da tsawon shekara da shekaru suka kafa gaba da abokan zamansu waɗanda suke kira "baƙi" a Kudancin Kaduna.

Ya ce Kudancin Kaduna yanki ne da ya ƙunshi garuruwa irinsu Zangon Kataf da Zankuwa da kuma Kafanchan, waɗanda mutane daga arewacin ƙasar irinsu Kano da Bauchi da sauransu, suka je suka zauna.

"Kamar Kafanchan, gari ne na reluwai wato mai tashar jirgin ƙasa, akwai mutane daga kudancin Najeriya, (wasu) daga arewacin Najeriya wa'nda sun (shafe) wajen shekaru ɗari a nan," in ji shi

Ya ce irin waɗannan mutane sun shafe gomman shekaru, wasunsu ma kakannin kakanninsu a Kudancin Kaduna aka haife su, amma 'yan asalin yankin sun ce mutanen baƙi ne don haka sai sun tashi.

Wannan layi ne
Rashin tabbatar da hukunci ga masu laifi

Elrufa'i ya ce tun bayan ɓarkewar rikicin 1980 a Kasuwar Magani, sai faɗa ya ci gaba da ruruwa kuma ake ta samun tashe-tashen hankula a jihar Kaduna.

"1992, an kashe fiye da mutum 1,300 a Zangon Kataf, wanda yawanci mutane ne....aka ce wai baƙi ne, rigima a kan kasuwa ta sa aka yi wa'yannan kashe-kashe".

Ya ce rikicin ya sa har gwamnatin Najeriya a zamanin mulkin Janar Ibrahim Badamasi Babangida ta hukunta wasu, amma daga baya aka sake su.

"To, wannan rashin yanke hukunci ga masu irin wannan ta'addanci, ya sa a kudancin Kaduna, mutane sun ɗauka cewa in ka kashe mutum, ko ka ƙona gidansa, ba abin da zai faru," cewar Elrufa'i.

Abin da muka gada ke nan, kuma wannan abu an daɗe ana yi, yanzu wurin shekara 40 ana wannan ya-ƙi-ci-ya-ƙi-cinyewa, domin an sa addini da ƙbilanci da tohuwar ƙiyayya ta shekara da shekaru, in ji gwamnan.

Jan ƙafa a shari'o'in da suka danganci rikicin

Malam Nasir Elrufa'i ya kuma bayyana takaici kan jan ƙafar da kotuna ke yi wajen yanke hukunci a shari'o'in da suka danganci rikicin kudancin Kaduna.

Ya ce sun kama mutane da yawa kuma sun gurfanar da su a gaban kotu tun cikin 2016, waɗanda ya ce har yau, ba a yanke hukunci ba.

"Kullum lauyoyi su samu wata hanya ta hana ci gaba da shari'ah, wani lokaci ma su kansu masu shari'ar ba su son su yi shari'ar. Har a wurin shari'ar akwai wa'yanda suke kawo son rai na addini da na ƙabilanci," gwamnan ya yi zargi

Ya ce ko a kwanan sai da gwamnatin jihar ta shigar da ƙorafi kan wata mai shari'ah da suka zarga da kawo cikas.

Wannan layi ne
Rashin ƙwarin gwiwa kan hukumomi

Gwamnan na Kaduna ya kuma ce Najeriya ba ta da yawan jami'an tsaron da za a iya turawa kowanne gida ko kowacce unguwa ko kowanne ƙauye a yankin, don haka ya buƙaci mutane su zauna lafiya da juna.

Idan mutane ba su zauna, sun yarda za su zauna lafiya ba, kuma in suna da matsala, su kai wa hukuma don a yi musu shari'ah. Kowa in ya ce in aka yi masa laifi sai ya rama. Wannan abu ba zai kawo zaman lafiya ba, Elrufa'i ya ce.

Ya ce abin da ke faruwa ke nan a yankin. "Su Fulani, idan aka yi musu laifi, ba za su faɗa ba. In aka kashe wani nasu, ba za su faɗa wa 'yan sanda. Sai su je su shirya su ce sai sun rama".

Su ma 'yan asalin yankin idan aka yi musu laifi, maimakon su faɗa wa hukuma, a bincika don gurfanar da mutanen da suke zargi a gaban kotu, sai su ce sai sun rama, a cewar gwamnan.

SOURCE: BBCHAUSA

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Duba Dalili biyar da ya sa rikicin Kudancin Kaduna ya-ƙi-ci-ya-ƙi-cinyewa"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?