LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Duba Abin da Sarkin Musulmi ya fada wa El-Rufa’i Yayin Ziyara

Aranar Litinin ne Sarkin Musulmi, Sultan Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya ziyarci Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rfufa’i a fadar gwamnatinsa.

Ziyarar Sarkin Musulmin na zuwa ne kwana da guda bayan da tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya yi makamanciyarta inda suka tattauna a kan batutuwan da suka shafi tsaro da tattalin arzikin jihar.

Sarkin Musulmi ya ziyarci El-Rufai
Yadda wakar Hausa ta Sambisa ta tayar da kura
El-Rufai: Majalisar Shari’a ta caccaki NBA
A yayin da Sultan ya kaurace wa hira da manema labarai bayan ganawarsu, Gwamna El-Rufai ya ce ziyarar da Sarkin Musulmin ya kawo tana da nasaba da kalubalen rashin tsaro da ya addabi Kudancin Jihar Kaduna da sauran sassan jihar.

Gwamnan ya yi bayanin cewa Sarkin ya gabatar masa da shawarwi kan matakan da za a ribata domin magance matsaloli na rashin tsaro da jihar take fuskanta.

Haka kuma gwamnan ya nuna yabawa da ziyarar da Sarkin ya kawo domin jaddada goyon bayansa wajen ganin zaman lafiya ya wanzu a jihar.

Sarkin Musulmin ya sauka a Gidan Gwamnatin Kaduna na Sir Kashim Ibrahim da misalin da azahar cikin wata bakar mota kirar Jeep.

Daga cikin tawagar da ta tarbi Sultan akwai Sakataren Gwamnatin Jihar, Balarabe Abbas; Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin Jihar, Muhammad Sani Dattijo da kuma Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na jihar, Samuel Aruwan.

Isowar Sarkin Musulmin fadar ke da wuya ya fada ofishin Gwamna El-Rufa’i inda suka shiga bayan labule tare da wasu kusoshin gwamnatin da ciki har da Sanatan Shiyyar Kaduna ta Arewa, Suleiman Abdu-Kwari.

SOURCE: AMINIYA DAILY TRUST 

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments