LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Daukar bindiga: ‘Yan sanda sun gayyaci mashawarcin Ganduje

Ofishin Rundunar ’Yan Sanda ta Kasa shiyya ta daya da ke Kano ta gayyaci mashawarcin Gwamnan Kano a kan Harkokin Siyasa Mustapha Hamza Buhari Bakwana bisa zargin yin barazana da bindiga tare da umartar magoya bayansa da su kashe abokan adawarsa.


A wani hoton bidiyo da ya karade gari dai an ga Bakwanan rike da karamar bindiga kirar fistol yana zuga magoya bayansa a lokacin taron Kwamitin Sulhu na Shugabannin Jam’iyyar APC a Karamar Hukumarsa ta Kumbotso.


A yayin zaman kwamitin wanda dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Mazabar Rano, Kibiya da Bunkure, Kabiru Alhassan Rurum yake shugabanta aka samu yamutsin da ya kai ga zubar da jini tsakanin magoya bayan Bakwana da wasu matasa.


Hakan ta sa shugabannin Jam’iyyar a Kumbotso rubuta takardar korafi ga Rundunar ‘Yan Sandan da Gwamna Abdullahi Ganduje da kuma Hukumar Kare Hakkin Dan Adam ta Kasa da su bibiyi lamarin don yi wa tufkar hanci.


Buhari Bakwana

A takardar korafin an zargi Mustapha Bakwana da fito da bindiga a bainar jama’a da kokarin tunzura magoya bayansa a kan abokan hamayyarsa.


Sai dai a martani, Bakwana ya musanta faruwar lamarin gaba daya inda ya ce makiyansa ne suka shirya hakan don bata masa suna.


A cewar Bakwana, “An ce na je wannan taro da magoya bayana wanann karya ne. Ni kadai na je wurin nan domin ko direba ban je da shi ba.


“Bayan na shiga na yi magana da Shugaban Kwamitin Alhassan Rurum sai na fito zan tafi sai wasu matasa suka fara yi min ihun ‘Ba ma yi ba ma yi’.


‘Hada bidiyon aka yi kamar na Dalar Ganduje’


“To ka san a Kumbotso na yi wa mutane alheri, hakan ya sa ire-iren matasan da na sama wa aiki suka mayar musu da martani.


“Amma ni babu wanda na sa ya daki wani ballantana ya kashe shi.


Har ila yau, Bakwana ya musanta batun bidiyon da ke yawo a kafafen sada zumunta inda ya ce makiyansa ne suka hada shi kamar yadda aka hada bidiyon Dalar Ganduje.


Kakakin Rundunar ‘Yan Sanda na Shiyya ta Daya, Rabi’u Ringim ya tabbatar cewa sun gayyaci Bakwana inda aka yi masa tambayoyi a kan zarge-zargen da aka yi masa na fito da bindiga tare da yin amfani da ‘yan daba wajen kai wa mutane hari tare da tayar da husuma.


SOURCE: AMINIYA DAILY TRUST

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments