--
Coronavirus: Dalilai uku da suka hana korona tasiri a Afrika

Coronavirus: Dalilai uku da suka hana korona tasiri a Afrika

 

A ranar Juma'a 14 ga watan Agustan 2020 ne aka cika wata shida da ɓullar cutar korona a Afrika inda aka samu mutum na farko da ya kamu a Masar cikin watan Fabrairu.


Kawo yanzu dai, fiye da mutum miliyan ɗaya ne suka kamu da cutar a nahiyar Afrika, kuma har yanzu ana samun ƙaruwar masu kamuwa da cutar a ƙasashen nahiyar.


Sai dai duk da haka, Hukumar Lafiya Ta Duniya ta ce ba a kai ga gano dalilan da suka sa nahiyar take da ƙarancin masu kamuwa da cutar ba idan aka kwatanta da sauran nahiyoyi na duniya.


Ƙasashe biyar da suka haɗa da Afrika Ta Kudu da Masar da Najeriya da Ghana da Aljeriya ne ke da kashi 74 cikin 100 na masu dauke da cutar ta korona a Afrika.


Alƙaluma dai sun nuna cewa a duniya kusan mutum miliyan 21 ne suka kamu da cutar, yayin da ta yi ajalin 660,00, to sai dai a Afrika mutum miliyan daya ne suka kamu, kuma mutum 24,000 suka mutu bayan kamuwa da cutar kamar yadda ƙididdiga ta nuna a ranar Juma'a.


Sai dai wasu masana na ganin akwai wasu dalilai na musamman da ya sa cutar ba ta yi tasiri a Afrika ba kamar yadda ta yi a sauran nahiyoyi.


Dakta Nasir Sani Gwarzo, wani ƙwararren likita ne kuma masani kan cutuka masu yaɗuwa, kuma ya bayyana wasu dalilai a ya ke ganin suka sa cutar ta korona ba ta yi wa ƙasashen Afirka kamun kazar kuku ba duk da a cewarsa ba a tabbatar da dalilan ba kimiyyance:

Yanayin zafi a nahiyar Afrika

Tun bayan ɓullar cutar koirona a duniya, an ta yaɗa jita-jita kan cewa rayuwa a wuri mai ɗumi kan iya kare mutane daga kamuwa da cutar korona, amma Hukumar Lafiya Ta Duniya ta fito fili ta ce hakan ba gaskiya bane.


Akasarin ƙasashen Afrika, ƙasashe ne da ke cikin yanayi na zafi, kuma a cewar Dakta Sani Gwarzo, "ƙasashe masu ɗumi sun ɗan fi samun rangwame". Dakta Gwarzo ya dogara ne da cewa gashi an yi wata shida da ɓullar cutar a nahiyar ta Afrika, amma adadin waɗanda suka mutu sakamakon cutar a nahiyar bai kai rabin na ƙasa ɗaya da ke a sauran nahiyoyi ba.


Yawan matasa a Afrika

Bincike da Hukumar Lafiya Ta Duniya ta gudana, ta ce matasa ba su tsira daga kamua da cutar korona ba. A cewar Dakta Gwarzo, "idan aka yi la'akari za a ga cewa matasa sun fi yawa a nahiyar Afrika, su kuma can za a ga akwai tsofaffi dayawa, wanda da cutar ta shiga, nan da nan za ta yi musu mummunar illa".


Yawan tafiye-tafiye na mutanen Turai

A tattaunawar BBC da Dakta Gwarzo, ya ce akwai yiwuwar cewa yawan tafiye-tafiye da sauran mutanen nahiyoyi ke yi ya sa cutar ta fi ƙamari fiye da Afrika.


"Yadda 'yan Afrika suke tafiye-tafiye, bai kai yawan yadda 'yan Turai suke tafiye-tafiye ba, yawan kasar da ta fi kowace yawan matafiya, na ƙasa da ƙasa sun fi samun wannan matsala".


Dakta Gwarzo ya ce duk da cewa waɗannan dalilian da ya bayyana ba a tabbatar da su a kimiyance ba, amma ana nan ana tantance su.


SOURCE: bbchausa/

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657




0 Response to "Coronavirus: Dalilai uku da suka hana korona tasiri a Afrika"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?