LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Biyan bashi: FG ta amince a biya ma'aikatan N-Power da aka sallama kudadensu

Minista Sadiya Umar Farouq ta amince da a biya ma'aikatan N-Power da aka sallama kudadensu, karkashin N-SIP

Sadiya ta bayyana cewa rukunin A da B na ma'aikatan N-Power sun riga da sun san cewa aikinsu na watanni 24 ne

Ministar ta kuma bayyana cewa wadanda suka nuna sha'awar shiga shirin a rukuni a C za a tantancesu tare da daukarsu ne bisa cancanta Ma'aiakatar jin kai da bunkasa rayuwa, karkashin Sadiya Umar Farouq ta amince da a biya ma'aikatan N-Power da aka sallama kudadensu, karkashin N-SIP.

A ranar Litinin 24 ga watan Agusta 2020, Ministar ta amince da abiya basussukan da tsofaffin ma'aikatan ke bi, wadanda ke a rukuni na A da B. Tuni dai aka tura bukatar biyan basussukan har zuwa watan Yuni, 2020 ga ofishin babban akanta na kasa domin kammala bincike da biyan kudaden.

A yanzu dai kudaden watan Yuli na wasu daga cikin 'yan rukunin B ne ba a kai ga biya ba, kuma bukatar na gaban ofishin akantan. Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga hadimin ministar ta fuskar watsa labarai, Nneka Ikem Anibeze da aka rabawa manema labarai a ranar Alhamis.

Sanarwar ta bayyana cewa masu cin gajiyar shirin 14000 da aka cire sunayensu daga ofishin AGF a yayin biyan kudin watan Maris zuwa Yuni 2020, na daga cikin wadanda manhajar GIPMIS ta ki karbar bayanan bankunan biyan kudinsu.

A cewar rahoton ofishin AGF, duk wani mai cin gajiyar shirin da ke karbar albashi daga gwamnati ba zai samu kudinsa ba. Ma'aikatar FMHADMSD ta bukaci wadanda abun ya shada da su gabatar da dalilan da ya sanya basu samu kudinsu ba daga ofishin AGF, inda ta sha alwashin yin mai yiyuwa wajen biyansu.

 Idan har kuwa basu samu kudadensu ba saboda wani kuskure na daban, to ma'aikatar ta bada tabbacin biyansu cikin karamin lokaci da zaran ofishin AGF ya gyara kuskuren. Minista Sadiya Farouq ta bayyana cewa rukunin A da B na ma'aikatan

N-Power sun riga da sun san cewa aikinsu na watanni 24 ne, don haka bai kamata a samu sabani ba don an sallame su. Kari da hakan, ma'aikatar ta ce a shekarar da ta gabata ne ta karbi ragamar shirin, kuma babu wani shiri na mayar da ma'aikatan su zama na din din din a gwamnatance.

Ministar ta kuma bayyana cewa wadanda suka nuna sha'awar shiga shirin a rukuni a C za a tantancesu tare da daukarsu ne bisa cancanta.

 SOURCE: LEGIT.NG

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments