LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Bidiyon faston Najeriya yana tada matacce ya janyo cece-kuce

Wani bidiyon faston Najeriya mai cike da abun mamaki da al'ajabi ya janyo cece-kuce a kafafen sada zumuntar zamani A bidiyon, an ga faston yana addu'a a kan wata mata da ta mutu har aka saka ta a akwatin gawa 

Bayan wani lokacin da ya shafe yana addu'a, an ga matacciyar matar ta tashi tsaye tare da fitowa daga akwatin gawar Wani faston Najeriya ya janyo cece-kuce bayan wani bidiyonsa ya watsu a kafafen sada zumuntar zamani, shafin linda Ikeji ya wallafa. 

A bidiyon mai cike da al'ajabi da abun mamaki, an ga faston yana tada wata mata da ta mutu a cikin cocinsa, inda ta mike garas bayan mutuwarta. An ga matar da farko a cikin akwatin gawa, inda aka rufe fuskarta da wani farin abu yayin da faston ke mata addu'a. 

An hango wasu daga cikin mambobin cocin suna rera wakoki daga bayan faston kafin daga bisani matar ta tashi daga cikin akwatin gawar. Hakan kuwa ya janyo cece-kuce mai tarin yawa a kafafen sada zumuntar zamani inda wasu ke kallon hakan a matsayin mu'ujizar bogi.

SOURCE: LEGIT.NG

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments