LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Bidiyo: Yadda aka kama wata budurwa 'yar aiki tana zubawa uwar dakinta fiya-fiya a cikin ruwan sha

Wani bidiyo da yake ta yawo a shafukan sadarwa ya nuna wata budurwar 'yar aiki da uwar dakinta ke tuhuma akan zuba mata guba da tayi a cikin ruwan da za ta sha Asirin wata budurwa 'yar aiki ya tonu, bayan an kamata tana shirin kashe uwar gijiyarta, 

budurwar dai an kamata tana zubawa uwar dakin nata guba a cikin ruwan sha. A lokuta da dama ana gargadin mutane akan hankali da irin yaran da zasu dinga daukowa a matsayin 'yan aiki. Sai dai kuma ance idan bera nada sata daddawa ma nada wari, 

domin kuwa a lokuta da dama suma iyayen dakin nasu suna da tasu matsalar, domin kuwa an sha samun bidiyo da rahotanni kala-kala akan yadda iyayen dakin irin wannan yara ke azabtar da su. 

Duk da dai ba a bayyana ainahin inda wannan lamarin ya faru ba, amma dai an tabbatar da cewa a Najeriya ne.

A cikin bidiyon wanda jaridar Linda Ikeji ta wallafa a shafinta na Instagram mai kimanin tsawon minti uku da yake ta yawo a shafukan sadarwa an jiyo matar tana tuhumar 'yar aikin nata wacce take zargi da zuba mata guba a cikin ruwan da za ta sha. 

A yayin da wasu 'yan Najeriya ke goyon bayan abinda matar ta yiwa 'yar aikin, wasu kuma suna zargin cewa akwai yiwuwar matar tana da laifi, tunda babu yadda za ayi ana zaman lafiya 'yar aiki tayi kokarin kashe uwar dakinta. 


Ga dai bidiyon yadda lamarin ya kasance: Idan ba a manta ba a cikin wannan shekarar ne dai aka kama wata mata da ta shafewa 'yar aikinta gaba da barkono, inda wannan lamari ya jawo kace-nace da yawa a shafukan sadarwa. Haka kuma duka a cikin wannan shekarar din aka sake kama wata matar ita ma da ta bugawa 'yar aikinta kusa a kanta. 

SOURCE: LEGIT.NG

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments