LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Bayan gayyatar DSS, Rundunar Ƴan sanda ta gayyaci Mailafia zuwa Abuja

Rundunar Ƴan sandan Najeriya ta gayyaci tsohon mataimakin shugaban gwamnan babban bankin Najeriya, CBN, Dr Obadiah Mailafia bisa wasu kalamai da ya furta yayin hira da aka yi da shi a gidan rediyo. 

Ƴan sandan za su fara binciken su ne duk da cewa hukumar ƴan sandan farin kaya, DSS, tana gudanar da nata binciken a kan tsohon mataimakin gwamnan CBN ɗin. Sai dai rundunar ta ƴan sanda ba ta ambaci dalilin gayyatar sa ba a cikin takardar da ta aike masa kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Mataimakin kwamishinan ƴan sanda, Umar Sanda ne ya saka hannu a kan wasikar a madadin mataimakin Sufeta Janar na ƴan sanda, sashin masu binciken manyan laifuka, CID, da ke Abuja. 

A takardar mai lamba 3000/X/FHQ/ABJ/VOI/245/8, mai ɗauke da kwanan wata 20 ga watan Agusta, ƴan sandan sun bukaci Mailafia ya zo ofishin hukumar sashin masu binciken manyan laifuka, Garki Area 10 Abuja a ranar Litinin 24 ga watan Agustan 2020 da karfe 11 na safe. 

Takardar mai laƙabin "Ayyukan bincike, Binciken ƴan sana'a tana ɗauke sa gargadin cewa abin sirri ta ke ɗauke da shi kuma duk wanda ya fallasa abinda ta ke ɗauke da shi zai iya fuskantar hukunci." Saƙon da ke jikin wasikar ya ce, "muna sanar da kai cewa wannan ofishin na bincike a kan wani lamari da sunan ka ya fito.

 "Saboda haka, muna gayyatar ka tattauna da mataimakin Sufeta Janar na Ƴan sanda, FCID Abuja a ranar Litinin 24 ga watan Agustan 2020 misalin ƙarfe 11 na safe a daki mai lamba 407, bene na uku a ginin FCID, Area 10 Garki Abuja." 

Tsohon mataimakin gwamnan na CBN wanda ya yi digirinsa na uku a Jami'ar Oxford da ke Birtaniya ya ce wasu tsaffin mayaƙan Boko Haram ne suka faɗa masa amma daga baya ya sassauta abinda ya faɗi. A halin yanzu dai Mailafia yana aiki ne a Cibiyar Nazarin Manufofi da Muhimman Buƙatu ta Ƙasa,

 NIPPS da ke Kuru. Da aka tuntube shi game da batun a wayar tarho a ranar Juma'a, Mailafia ya ƙi cewa majiyar Legit.ng komai inda ya ce su tuntubi lauyansa. 

SOURCE: LEGIT.NG

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments