LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Batanci ga Allah: Kotu ta yanke wa yaro mai shekaru 13 hukunci mai tsanani

Hukumar kula da lamurran addinai da 'yancinsu na Amurka, ta caccaki hukuncin shekaru 10 da aka yankewa yaro mai shekaru 13 a gaban wata kotun shari'ar Musulunci da ke Kano. Yaron mai suna Umar Faruk, an kama shi da laifin yin kalaman batanci ga Allah a yayin da suke muhawara da wani abokinsa. 


An kama shi da laifin kuma an yanke masa hukunci ne a ranar 10 ga watan Augusta, rana daya da aka yankewa mawakin Kano da ya yi wa Annabi Muhammadu kalaman izgili. Hakazalika, alkali daya, Aliyu Kanu ne ya yankewa Yahaya da Faruk hukuncin a kotun shari'ar Musulunci. Hukumar ta kushe dukkan hukuncin don ta ce hakan ya take hakkinsu na dan Adam. 


Hukumar kula da lamurran addinai da 'yancinsu na duniya (USCIRF) ta kushe dokokin batancin na Najeriya. USCIRF kungiya ce mai zaman kanta kuma ba ta siyasa bace wacce aka kafa a Amurka don dubawa tare da rahoto a kan duk wata barazana ga 'yancin addini. 


A wata takarda da hukumar ta yi martani a kan hukuncin, ta kushe hukuncin kisan da aka yanke wa Sharif-Aminu a kan kama shi da aka yi da laifin batanci ga Annabi Muhammad. Kwamishinan USCIRF, Frederick Davie, ya ce, 


"Abun takaici ne yadda Sharif-Aminu ke fuskantar hukuncin kisa a kan bayyana abinda ya yarda da shi ta hanyar waka. "Majalisar dattawan Amurka ya kamata ta yi gaggawar duba lamarin tare da kira ga gyara dokokin batanci." Hannibal Uwaifo, shugaban kungiyar lauyoyin Afrika, ya kushe hukuncin kuma ya ce hakan bai yi biyayya da kundin tsarin mulki ba. Uwaifo ya ce, 


"Ina kira ga antoni janar na tarayya da ya shiga lamarin kuma ya hana irin wannan kotun hukunci a Najeriya. "Wannan kasa ce da ake satar biliyoyin naira kuma ake basu wani bangarensa don goyon baya. Daga nan sai a ce mutum ya yi batanci amma ga addinin. "A daina yankewa matasa da kananan yara irin wannan hukuncin. Ina tunanin dole a daina domin abun dariya ne." 

SOURCE: LEGIT.NG

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments