LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Bahaushiya yar Gombe ta fantsama yanar gizo neman mijin aure

Wata matashiyar Bahaushiya da ke tsananin neman mijin aure ta je dandalin soshiya midiya domin gwada sa’arta -

 Matashiyar budurwar mai suna Salmerh Umar ta ce ita ‘yar jihar Gombe ce - Salmerh ta ce ba za ta iya ci gaba da boye yadda take ji ba, inda ta bukaci ‘yan Najeriya da su taya tad a addu’a Wata matashiyar budurwa Bahaushiya da aka ambata da suna Salmerh Umar ta je shafin zumunta

domin neman mijin aure yayinda ta bukaci ‘yan Najeiya a Twitter da su taya tad a addu’a. Matashiyar budurwar wacce shafinta na Twitter yake a matsayin @SalmerhUmar ta ce ba za ta iya ci gaba da boye yadda take ji a ranta ba.

Salmerh wacce ta kasance ‘yar jihar Gombe, ta wallafa hotunanta guda biyu a shafin nata domin nuna wa mutane irin kyawun da Allah ya yi mata.

Shakka babu matashiyar na so ta dandani zuman da ke cikin aure sannan ta bar duniyar yan matanci.Wallafar da ta yi ya sa mutane da dama yin sharhi inda suka dunga fadin albarkacin bakunansu. Wasu daga cikin masu sharhin sun nuna ra’ayinsu na son mallakar budurwar a matsayin matarsu, cewa suma a kasuwa suke. Har ta kai wani ya ma ajiye lambar wayarsa, inda ya bukaci da ta kira shi.
Wani mai amfani da shafin Twitter ya bukaci da ta duba halayya sosai domin tana da kyau da bai kamata ace bata da mashinshini ba.

 SOURCE: LEGIT.NG

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments