LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

An yanke wa direba daurin rai-da-rai a kan Fyade

Kotu ta yanke wa wani direban babur mai kafa uku hukuncin daurin rai-da-rai bayan ya yi wa yarinya mai shekaru 14 fyade, tare da sanya mata cutar hanta ta Hepatitis B.

Babbar Kotun da ke zamanta a garin Akure, Jihar Ondo ce ta yanke wa mutumin hukuncin a ranar Litinin, 10 ga Litinin Agusta bayan shafe shekara biyu tana sauraron karar.

Da yake yanke hukuncin, alkalin kotun, Mai Shari’a Bode Adegbehingbe ya ce hujojjin da aka gabatar sun tabbatar cewa wanda ake tuhuman ya aikata laifin.

A ranar 12 ga watan Yulin shekarar 2018 ne Blessing Kingsley ya dauki yarinyar a babur dinsa mai kafa uku cewa zai rage mata hanya a lokacin da ya hadu da ita ta fito sayen wani abu a garin Ondo.

Maimakon ya sauke ta inda za ta yi sayayya sai ya zarce da ita gidansa ya ce ta je ta gaishe da iyalinsa inda ya yi mata fyade, lamarin da ya sa aka yi karar sa a ofishin ‘yan sanda da ke yankin Fumbi Fagun.

A lokacin  binciken likitoci ya tabbatar an yi wa yarinyar fyade, kuma an samata cutar Hepatitis B.

A wancan lokacin aka kama shi aka gurfanar da shi a gaban mai shari’a Bode Adegbehingbe da laifin fyade wanda ya saba dokar manyan laifukn jihar na sashe 358 na shekarar 2006.

Wanda ake tuhuman a wancan lokacin shi kadai ya shaidi kansa sai lauya guda da ya tsaya masa.

A daya bangaren kuma mai gabatar da karar ya gabatar da shaidu hudu da suka hadar da wacce aka yi wa fyaden da dan sandan da ya kama wanda ake zargi, Sajen Olanrewaju Agbelusi, sai wanda ya dauki hoto da kuma likintan da ya yi bincike.

Wanda ya shigar da karar ya kuma gabatar da hujojjin da suka hadar da tufafin yarinyar dauke da jini a jikinsu, da hoton wajen da aka yi mata fayde, dauke da jinin da ya fantsama a kan katifa, da kuma takardar sakamakon binciken likitoci.

Duba da hojojjin da mai shigar da karar ya gabatar, alkalin kotun, Mai Shara’a Adegbehingbe ya tabbatar da laifin fyade ga wanda ake tuhuma ya kuma yanke masa da hukuncin daurin rai-da-rai.

SOURCE:  AMINIYA DAILY TRUST

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments