--
An tsare Dan Majalisa a kurkuku kan garkuwa da mutane

An tsare Dan Majalisa a kurkuku kan garkuwa da mutane

Wata kotu ta tsare Dan Majalisa mai wakiltar Katsina Ala ta Yamma a Jihar Benue bisa zarginsa da fashi da kuma garkuwa da mutane.


Kotun Majistaren ta tsare Dan Majalisar Dokokin Jihar Benue Jonathan Agbidye a gidan yarin ne bayan an gurfanar da shi a ranar Juma’a.


Mai Shari’a Isaac Ajim ya ba da umarnin tsare Agbidy dan jam’iyyar APC ne tare da wanda ake zarginsu tare.


Dan sanda mai gabatar da kara Fidelis Ogbobe ya shaida wa kotun cewa a ranar 22 ga watan Mayun 2018 an yi fashin wata motar a-kori-kura kirar Hilux da wasu kayan cikinta da bakin bindiga a hanyar Katsina-ala zuwa Tordonga a Karamar Hukumar Katsina-ala.


Ya ce wadanda ake zargi da kwace motar motar mallakin shirin kula da lafiya na Apin, sun kuma yi garkuwa da jami’an lafiyar wanda kowanne daga cikinsu babban laifi ne.


Jami’in ya ce daga baya ‘yan sanda suka kama Agbidye da abokin harkarsa a Makurdi da motar sun canza mata lamba.


Mutanen biyu da wasu biyu da suka tsare, a cewarsa, sun hada baki ne kuma ‘yan fashi ne da kuma garkuwa da mutane karkashin gawurtaccen mai garkuwa da mutane, Terwase Akwaza (Ghana) wanda ake nema ruwa a jallo.


Zaman kotun bai kai ga sauraron bayanan bangarorin biyu ba.


Lauya mai gabatar da kara ya shaida wa kotun cewa ana kan binciken mutanen don haka ya nemi karin lokaci domin a kammala.


Lauyan wadanda ake bai ja da bukatar ba amma ya ce nan gaba zai gabatar da bukatar karbar su beli.


Mai Shari’a Ajim ya dage sauraron karar zuwa 12 ga watan Oktoba 2020, yayin da aka wuce da dan majalisar da abokinsa zuwa Babban Gidan Yarin Tarayya da ke Makurdi.


SOURCE: AMINIYA DAILY TRUST

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "An tsare Dan Majalisa a kurkuku kan garkuwa da mutane"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?