--
Abdullahi Ganduje: Dattawan Kano sun kai ƙararsa wajen Buhari

Abdullahi Ganduje: Dattawan Kano sun kai ƙararsa wajen Buhari

Wata gamayyar kungiyoyi da ke rajin kare mutuncin mutanen Kano ta kai ƙarar Gwamnan jihar Abdullahi Ganduje ga Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari kan yunƙurinsa na ciyo bashi daga wani bankin China domin gina hanyar jirgin ƙasa.

Gamayyar kungiyoyi fiye da 15 ƙarƙashin inuwar Kano Forum ta bayyana abin da ta kira katafaren bashin da gwamnatin Ganduje ke son karɓowa domin gina kashin farko na hanyar jirgin ƙasa a birnin Kano a matsayin abin da ba shi da amfani ganin manyan kalubalen da ke gabanta.

Kungiyar ta yi zargin cewa Gwamna Ganduje zai ciyo bashin euro miliyan 684, wato kimanin naira biliyan dari uku wanda suka ce sai an shekara 50 gwamnatin ba ta gama biyan bashin ba.

Shugaban kungiyar Alhaji Bashir Othman Tofa ya ce: "Abu ne da kusan ba zai yiwu ba a ce jihar Kano ta ɗauki nauyin wani bashi fiye da wanda aka riga aka jibga ma ta a baya."

A cewarsa, za su gurfanar da gwamnan a kotu idan ya zaɓi ci gaba da shirin karɓo bashin.

"Wannan gamayyar za ta kuma bi duk wata hanyar da dokar ƙasa ta samar domin hana gwamnatin ta Kano aiwatar da aikin samar da hanyar jirgin ƙasa a Kano," a cewar takardar da kungiyar ta fitar.

Kungiyar ta ce ciyo bashin zai jefa al'ummar Kano cikin kuncin rayuwa tana mai cewa maimakon gina layin dogon, kamata ya yi gwamnati ta yi amfani da irin wannan bashi wajen kara ajujuwa da samar da kayayyakin karatu, da kewaye makarantun jahar.

Sai dai Kwamishina watsa labarai na jihar ta Kano, Muhammad Garba, ya ce ba za su fasa ciyo bashin ba.

Ya kara da cewa kungiyar ta tsirarun mutane ce kuma ba da yawun al'ummar Kano take magana ba.

Rahotanni sun ce batun karbo bashin na cikin manyan abubuwan da suka sanya Gwamna Ganduje ya sauke tsohon sarkin Kano daga kan kujerar mulki sakamakon sukar da ya yi masa a kan shirin.

A kwanakin baya 'yan kungiyar Kwankwasiyya da ke goyon bayan tsohon gwamnan Kano Raib'u Kwankwaso, sun kai kai karar gwamanan na Kano abdullahi Umar Ganduje kotu inda suka nemi ta dakatar da shi ciy bashin na naira biliyan dari uku daga kasar ta China.

SOURCE: BBCHAUSA

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Abdullahi Ganduje: Dattawan Kano sun kai ƙararsa wajen Buhari"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?