--
A raba ni da matata Amina domin ta yi kokarin sanya mani guba – Magidanci ya sanar da kotu

A raba ni da matata Amina domin ta yi kokarin sanya mani guba – Magidanci ya sanar da kotu

Kotu ta rushe auren shekaru 14 tsakanin wani mai suna Dauda Saliman da matarsa Amina, kan zarginta da yunkurin ba mijinta guba

Alkalin kotun, Cif Ademola Odunade da wasu masu sasanci biyu sun ce an rushe auren ne domin wanzar da zaman lafiya a tsakani

An kuma mika ragamar kula da yaran a hannun mahaifiyarsu, inda mahaifinsu zai ci gaba da daukar dawainiyarsu Wata kotun gargajiya da ke zama a Mapo, Ibadan a ranar Talata, 25 ga watan Agusta, ta rushe auren shekaru 14 tsakanin wani mai suna Dauda Saliman da matarsa Amina,

kan zarginta da yunkurin ba mijinta guba. Shugaban kotun, Cif Ademola Odunade da wasu masu sasanci biyu sun ce an rushe auren ne domin wanzar da zaman lafiya a tsakani. Ya mika ragamar kula da yara uku da suka aifa a auren ga wacce ake kara wato mahaifiyarsu kenan, jaridar The Nation ta ruwaito.

Har ila yau ya umurci wanda ke karan wato mijin kenan da ya dunga biyan N15,000 a matsayin kudin abincin yaransa duk wata sannan kuma shine zai dunga daukar dawainiyar karatunsu da sauran harkokinsu.

Odunade ya nuna bacin rai a kan halayyar Amina na barin mijinta ya koma otel da kwana tsawon shekaru uku ba tare da ta koka a kan hakan ba. Ya bayyana cewa ita ce umul-aba’isin abunda duk ya same ta. A wani labarin, wani malamin addini, Adebayo Bamidele, ya roki kotun gargajiya da ke zama a Mapo,

Ibadan, da ta rushe aurensa na shekaru 17 da matarsa Felicia, kan hujjar cewa tana lalata masa harkoki. Bamidele ya fada ma kotun a ranar Talata cewa matarsa na aikata abubuwan da ke lalata masa kiran da yake zuwa ga Ubangiji.

“Tana yi mun zarge-zarge masu lalata suna a gaban mabiyana. “Ta mayar da ni mara aikin yi. “Duk mabiya na sun bar coci na,” in ji shi. Faston ya ci gaba da fada ma kotun cewa wasu mambobin cocin sun nakada masa dukan tsiya biyo bayan zarge-zargen da Felicia ta yi a kansa.

 “Felicia ta fada masu cewa ina amfani da bakaken aljanu da sihiri wajen kwashe masu arzikinsu. “Sun yi mun mugun duka, sun yaga mun kayana. “Har na kusa mutuwa. “A yanzu tana ikirarin cewa cocin nata ne. “Maganar gaskiya shine mun hada kudi wajen gina cocin, na rasa hanyar samuna saboda mugun nufinta a kaina,” in ji shi.

SOURCE: LEGIT.NG

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "A raba ni da matata Amina domin ta yi kokarin sanya mani guba – Magidanci ya sanar da kotu "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?