--
A cikin sabon bidiyo, Shekau ya yi wa Shettima, Zulum, Monguno, Bukarti da Dalung barazana

A cikin sabon bidiyo, Shekau ya yi wa Shettima, Zulum, Monguno, Bukarti da Dalung barazana

Shugaban kungiyar masu tayar da kaya ta Boko Haram, Abubakar Shekau, ya saki sabon bidiyo wanda ke barazana ga tsoho da kuma gwamnan jihar Borno na yanzu, Kashim Shettima da Babagana Zulum.

Haka kuma Shekau ya ja kunne mai ba da shawara kan harkokin tsaro na kasa, Babagana Monguno da manazarci kan kungiyoyi masu tsattsauran ra’ayi, Bulama Bukarti da tsohon Ministan Matasa da Wasanni, Solomon Dalung.

A cikin faifan bidiyon na tsawon mintuna 56, Shekau ya fassara taken Najeriya da taken Hukumar bautar kasa ta NYSC zuwa harshen Larabci, Hausa da kuma Kanuri. Ya yi ikirarin cewa duk musulman Najeriya da suke karanta taken, to ba masu Imani bane kuma sun cancanci a kashe su.

Ya tafi a kan cewa, duk Musulmin da ya karanta taken Najeriya a makaranta ko a wani wurin na daban, to kafiri ne ko da kuwa yana Sallah ya na Azumi.

A rukunin harshen Kanuri na bidiyon kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito, Shekau ya yi wa mutanen barazana wanda kusan dukkaninsu sun kasance ‘yan kabilar Kanuri. Ya kiraye su da sunayensu daya-bayan-daya, tare da gargadin cewa duk wanda ya karanta taken Najeriya “ko da kuwa da wasa, to ya zama kafiri walau yana Sallah da azumi.

” Wannan sabon bidiyo ya fito ne a yayin da a baya bayan nan kasar Amurka ta yi gargadin cewa, kungiyar Boko Haram ta fara fadada shinge daga yankin Arewa maso Gabas zuwa Arewa maso Yamma. A wani bidiyon da shugaban ‘Yan ta’addan kungiyar Boko Haram ya fitar kwanan nan, an ji ya na gargadin Bulama Bukarti tare da wasu shugabannin gwamnati da Sojojin Najeriya.

Abubakar Shekau ya kuma ja kunnen Ministan sadarwa na Najeriya, Isa Ali Ibrahim Pantami da shugaban kasa Muhammadu Buhari da Shugaban hafsun Soji, Janar TY Buratai. Bulama Bukarti wanda Masanin shari’a ne kuma Mai karatun Digirinsa na uku watau PhD a Jami’ar SOAS ta Ingila, ya fito ya maida martani bayan jawabin Abubakar Shekau.

Audu Bulami Bukarti ya nuna cewa ya san dalilin da ya sa ya zama kayar-bayan ‘Yan kungiyar ta’addan Boko Haram. Audu Bukarti ya yi wannan jawabi ne a shafinsa na Tuwita. A cewar Malam Bulama Bukarti wanda bincikensa daga cibiyar Tony Blair ta Duniya su ka zagaye ko ina, ‘

Yan Boko Haram su na kokarin toshe bakinsa ne, wanda ba zai yiwu ba. Duk da wannan barazana, Bulama Bukarti ya bayyana cewa ba za a taba tursasa masa ya yi gum ba, hakan ya na nufin zai ci gaba da magana a kan ‘Yan ta’addan na Boko Haram.

SOURCE:LEGIT.NG

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "A cikin sabon bidiyo, Shekau ya yi wa Shettima, Zulum, Monguno, Bukarti da Dalung barazana "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?