--
Wata sabuwa: An fara shirye-shiryen tsige wani gwamnan APC a Najeriya

Wata sabuwa: An fara shirye-shiryen tsige wani gwamnan APC a Najeriya



An fara sabin shiri na tsige Sanata Hope Uzodinma daga kan kujerar gwamnan jihar Imo a babbar kotun tarayya dake Abuja, kamar yadda Daily Sun ta ruwaito.

Jam’iyyar adawa ta Reform and Advancement Party (RAP), da kuma dan takarar gwamnanta da ya fito takara a zaben 2019 a jihar Okere Kingdom, sune suka kai wannan kara gaban kotun.

Kingdom da jam’iyyarsa sun bukaci kotu tayi bayani akan cewa shin jam’iyyar APC ce ta goyi bayan Uzodinma a wannan zabe da aka yi a baya?

Masu mika karar sun bukaci kotu da ta sanya hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta akan ta kwace takardun da ta bawa gwamnan na lashe zabe ta mika shi ga dan takarar jam’iyyar PDP, Emeka Ihedioha a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar.

An mika karar ne game da hukuncin kotun koli na daukaka karar mai lamba: SC/1384/2019, wacce ta amince da hukuncin kotun daukaka kara da kuma babbar kotun tarayya akan ta tabbatar da Ugwumba Uche Nwosu a matsayin wanda ya lashe zabe a shekarar 2019 a jihar Imo a karkashin jam’iyyar APC.

A cikin sammacin da suka aika wanda aka sanya a ranar Asabar 25 ga watan Yuni, mai lamba FHC/ABJ/CS/677/2020, masu shigar da karar sun gabatar da tambayoyi masu yawa akan hukuncin da kotu ta yanke.

Idan ba a manta ba dai kotun koli dake Abuja ita ce ta bayyana Uzodinma a matsayin wanda ya lashe zaben jihar ta Imo a shekarar da ta gabata.

Tun daga wannan lokacin dai gwamnan ya dinga fama da ‘yan adawa wadanda hukuncin kotun bai yi musu dadi ba.


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Wata sabuwa: An fara shirye-shiryen tsige wani gwamnan APC a Najeriya"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?