LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Matsalar Fyade: Sharrin Miyagun Malamai Da Rashin Ayyukan Yi Ne Yake Jawo Yawaitar Fyade A Nijeriya, Cewar Sheik Sani Sheriff Bichidibar ma'ikata sama da dubu 700 zai rage yawaitar fyade, cewarsa

Daga Shafin Rariya Tareda  Abdulrashid Abdullahi, Kano 

Shugaban majalisar malamai na kungiyar Izalah reshen jihar Kano, Sheikh Sani Sheriff Umar Bichi yace yawancin abubuwan da suke jawo mummunar ta'addancin na aikita fyade Shine sakaci na iyayen yara da kuma talauci na mutane da sharrin miyagun malamai.

Ya kara da jan hankalin Gwamnati da ta kara duba halin da mutane suke ciki ta tausasawa jama'a.

Malam ya kuma yi kira ga Gwamnatin Nijeriya da ta daure wajen daukar aikin nan da za ta yi kuma a dauki matasa da yawa a ba su aikin yi wannan zai rage yawan matasa marasa aure mata da maza.

Malam ya bada misali da jihar Kano, inda ya ce ida aka dauki matasa a kowacce karamar hukuma na jihar Kano idan aka dauki matasa dubu daya aka basu aiki kuma mutum dubu dayan nan kowanne ya yi aure ka ga a jihar Kano an rage 'yan mata da samari marasa aure mutum dubu arbain da hudu (44000)a jihar.

Kuma a ce kowacce jiha ta yi haka a kowacce karamar hukuma za a rage yawan fyade a kasar da izinin Allah.

Malam ya yi kira ga iyaye da su rage kudin aure dan 'yan matan su samu su yi aure. Kuma a tsaya akan shari'ar Allah akan maganar aure wannan shi ma zai rage matsalar fyade.

Daga karshe Malam ya yi addu'o'i ina zaman lafiya a Nijeriya da ma jihar Kano da suran kasahen musulmai.


 KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
 LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments