--
Mata mai juna biyu ta datse mazakutar mijinta da wuka a Taraba

Mata mai juna biyu ta datse mazakutar mijinta da wuka a Taraba



Wata matar aure mai shekara 25 da datse mazakutar mijin ta a garin Tella da ke karamar hukumar Gassol ne jihar Taraba. Matar mai suna, Halima ta tafka wannan aika-aikan ne a ranar Talata yayin da mijin ta, Umar Aliyu ke sharbar barci.


Kanin wanda abin ya faru da shi, Shagari Umar, ya ce ihun Aliyu ne ya jawo hankulan mutane inda suka zo suka tarar da shi kwance cikin jini. Umar ya yi ikirarin cewa, "Mun ga matarsa Halima zaune a gefen gado rike da wukar da ta yi amfani da shi wurin datse mazakutar dan uwanmu."


Ya kara da cewa kiris ya rage fusattaun yan uwan Umar da makwabta suyi mata duka amma, "manya sun shiga tsakani sun ce a tausaya mata saboda tana dauke da juna biyu kuma suka kira 'yan sanda."

A cewarsa, an garzaya da Aliyu zuwa Cibiyar Lafiya ta Tarayya, FMC, da ke Jalingo mai nisar kilomita 150 daga garin Tella. Ya ce, da isarsu asibitin, an bawa Aliyu kulawa cikin gaggawa aka tsayar da jinin da ke zuba daga raunin bayan an masa tiyata.


Likitan da ya kula da Aliyu, Dr Kyantiki Peter Adamu, ya shaidawa Daily Trust cewa an kira shi sashin wadanda ke bukatar kula cikin gaggawa don wani majinyaci da aka kawo bayan datse masa mazakuta. "Abinda muka yi shine tsayar da zubar jinin cikin gaggawa da kuma yi masa tiyata a inda aka masa rauni saboda ya rasa jini sosai kafin a kawo shi," in ji shi.

Ya ce bisa ga dukkan alamu majinyacin zai murmure amma yan uwansa sun bukaci su tafi da shi saboda haka babu abinda asibitin zai yi a kai. Shagari ya shaidawa majiyar Legit.ng cewa sun dauke Aliyu daga FMC Jalingo ne domin su tafi da shi wani asibiti a Gombe.

Mun dauke dan uwan mu daga FMC Jalingo mun tafi da shi FMC Gombe domin ya kara samun kulawar da ya ke bukata," in ji Shagari. Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, DSP David Misal ya tabbatar da afkuwar lamarin, ya kara da cewa 'yan sanda sum kama Halima sun kuma fara bincike.

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
 LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Mata mai juna biyu ta datse mazakutar mijinta da wuka a Taraba "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?