--
Hana Bara: Babu wanda ya isa ya hana Almajiranci - Sheikh Dahiru Bauchi

Hana Bara: Babu wanda ya isa ya hana Almajiranci - Sheikh Dahiru Bauchi



Shararren shehin Malami, Fadilatus-Shiekh Dahiru Usman Bauchi, ya bayyana rashin amincewarsa da gwamnonin Arewa bisa kokarin hana almajiranci da suke yi. A hirar da jaridar The Sun tayi da shi, Sheikh Dahiru ya ce ana kokarin takewa mutanen da sukayi imani da shirin almajiranci hakkinsu kuma yana daya daga ciki.

Shehi ya ce kundin tsarin mulkin Najeriya ta baiwa kowani dan kasa daman zuwa inda yaga dama domin yin addinin da yaga dama. Yace: "Kundin tsarin mulkin kasa ta bamu yancin yin addininmu duk yadda muka ga dama. Abinda mukafi girmamawa a addini shine AlKur'ani."


"Tun da addini ta basu dokokin da za'a bi amma suka ki biyayya, shin wani hakki suke da shi na baiwa Alkur'ani umurni? saboda haka, ba zamu yarda da haramta Almajiranci da gwamnonin Arewa sukayi ba."

"An take mana hakkin yancin yin addininmu. Ba zamu amince a take mana hakkin zuwa kowani waje a kasar nan domin aiwatar da addininmu ba." "Dalilin shine akwai gwamnati, kuma gwamnati na biyayya ne ga kundin tsarin mulki. Kundin mulkin tarayyar Najeriya ta baiwa ko wani dan kasa daman zuwa duk inda yaga daman yin addininsa.

 Almajirai yan Najeriya ne." "Kwashe mana mutane tamkar dabbobi da kaisu wurare daban-daban da ake yi, ba zamu amince ba. A matsayinmu na yan Najeriya, muna da hakkin yin addinimu. Alkur'ani ce abin farko a addinmu." "Ba zamu amince a hana almajiranci ba. Muna da hakkin zuwa ko ina a duniya domin karanta Alkur'ani."

Sheikh Dahiru Bauchi ya kara da cewa gwamnonin basu nemi shawarasa ba kafin haramta Almajirancin. Za ku tuna cewa kungiyar gwamnonin Arewa karkashin jagorancin gwamnan jihar Plateau, Simon Lalong, ta yanke shawarar mayar da Almajirai jihohinsu na asali tare da haramta almajirancin gaba daya a Arewacin Najeriya.

Gwamnonin irin na Kano, Kaduna, Nasarawa, da Neja tuni sun alanta haramcin Almajirancin a jihohinsu A jihar Kano, akalla Almajirai 193 ne suka kamu da cutar COVID-19. Hakazalika a jihar Kaduna da Abuja an samu da dama dauke da cutar.



KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
 LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Hana Bara: Babu wanda ya isa ya hana Almajiranci - Sheikh Dahiru Bauchi "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?