Duba Dalilin da yasa Jonathan ya ziyarci Buhari a Villa
Tuesday, 21 July 2020
Comment
![]() |
| Dalilin da yasa Jonathan ya ziyarci Buhari a Villa Source: UGC |
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, zai tuntubi sauran shugabannin kasashen nahiyar Afrika a kan yadda za a samu zaman lafiya mai dorewa a kasar Mali mai fama da rigingimu daban - daban.
Buhari ya bayyana hakan ne bayan karbar rahoto daga wurin wakilin zaman lafiya na musamman da aka tura kasar Mali, tsohon shugaban kasar Najeriya, Goodluck Jonathan.
A cewar wani jawabi da kakakin shugaban kasa, Femi Adesina, ya fitar a fadar gwamnatin tarayya da ke Abuja, ya ce Jonathan ya samu rakiyar shugaban kungiyar ECOWAS, Mista Jean-Claude Kassi Brou.
"Za mu tattauna da shugaban kasar Nijar, wanda shine ciyaman na ECOWAS, domin ya gabatar mana da jawabi, daga nan kuma za mu san menene mafita,"
a cewar shugaba Buhari. Buhari ya mika godiyarsa ga Jonathan a kan yadda ya bayar da lokacin wajen zuwa kasar Mali a matsayin wakili na musamman domin ya gano halin da take ciki dangane da batun tsaro.
Zanga - zangar neman shugaban kasar Mali, Ibrahim Boubacar Keita, ya sauka daga kan mulkinsa duk da yana da sauran shekaru uku a cikin biyar na zangon mulkinsa na biyu, ta rikide zuwa rikici
Wata kungiyar 'yan tawaye mai suna 'M5' ta bukaci a rushe kotunan kasar Mali da kundin tsarin mulki ya kafasu, sannan shugaba Keita ya yi murabus matukar ana bukatar samun lafiya a kasar.
Rikici ya barke bayan kotunan kasar Mali sun kwace kujerun mambobin majalisa 31 tare da mikasu zuwa hannun wasu 'yan takara da aka bayyana sun fadi bayan kada kuri'a. Kungiyar 'M5' ta yi zargin cewa kotunan sun aikata hakan ne bisa umarnin shugaba Keita.
Kungiyar ECOWAS ta yanke shawarar shiga rikicin kasar Mali bayan al'amura sun kara dagulewa a 'yan kwanakin baya bayan nan sakamakon kashe wasu masu zanga-zanga da jami'an tsaro su ka yi a ranar 10 ga watan Yuli.
Source: LEGIT.NG
TALLA: Sayi datar kowane network kamar: MTN, AIRTEL, GLO 9MOBILE mai inganci da rahusa latsa nan↓↓↓
Data Bundle Promo By BZ GLOBAL SERVICES
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Duba Dalilin da yasa Jonathan ya ziyarci Buhari a Villa "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?