LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Ba za su taba tuba ba, FG ta daina asarar kudinta a kan tubabbun Boko Haram - Sanata Ndume


Sanata Ali Ndume, shugaban kwamitin majalisar dattawa a kan harkokin sojojin kasar nan, ya soki yadda ake karbar tubabbun Boko Haram tare da mayar da su cikin jama'a. A makon da ya gabata, hukumar sojin Najeriya ta sako tubabbun 'yan ta'addan Boko Haram 601 bayan sun kammala shirin wayar musu da kai bayan sun tuba,

wanda rundunar Operation Safe Corridor ke shiryawa. A wata tattaunawa da ya yi da BBC Hausa a ranar Laraba, 29 ga watan Yuli, Ndume wanda ke wakiltar mazabar Borno ta Kudun, ya ce jama'arsa basu amince da gyaran hali da ake wa tubabbun 'yan Boko Haram ba.

Kamar yadda yace, mayakan ta'addancin ba za su taba sauya miyagun halayensu ba kuma ba za su tuba ba. A yayin caccakar shirin, Ndume ya ce "Jama'ata basu amince da wannan shirin ba. Abinda ya fi shine a bar shi kawai. "Ba wai hakuri suke bai wa jama'a ba, gwamnati suke bai wa hakuri tare da tunanin cewa sun gaza.

Daga nan ake karbarsu tare da tarairayarsu," yace. Ya kara da cewa, "Da yawa daga cikin wadanda suka tuban, guduwa suke yi su koma. Gwamnatin ta san abun yi kawai. Bai kamata a sake kawo maka wanda ya kashe maka iyaye ba ko 'yan uwa. "Idan akwai gaskiya a cikin al'amarin, wadanda ke sansanin 'yan gudun hijara ne ya kamata a horar wurin sana'a ta yadda za su fara sabuwar rayuwa."

A wani labari na daban, ‘yan gudun hijira 674 da suka dawo gida a garin Damasak sun samu tallafin kayayyakin abinci da kudi daga wurin gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum a ranar Asabar yayin da ya kai musu ziyara har Damasak, babban birnin karamar hukumar Mobar ta jihar.

Jama’ar da suka dawo Damasak din ‘yan gudun hijar ne daga jamhuriyar Nijar. Sun tsere ne sakamakon harin mayakan ta’addanci na Boko Haram. Zulum ya duba yadda ake raba hatsi da kayayyakin hadin abinci ga kowanne gida. Bugu da kari, ya bada umarnin rarraba N10,000 ga kowanne gida don ko ta kwana.

Gwamnan ya samu rakiyar kwamishinan ayyuka da gyara na jihar, yayin da suka gangara don duba ginin gidaje 1,000 da ake yi don wadanda suka dawo daga gudun hijirar su samu matsuguni.

SOURCE: LEGIT.NG
T
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments