LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Allahu Akbar: Hadarin mota ya kashe Yusuf Chinedozi Nwoha a hanyar KogiA ranar Laraba, 29 ga watan Yuli, 2020, musiba ta aukawa majalisar NSCIA ta kolin addinin musulunci a Najeriya. Malam Yusuf Chinedozi Nwoha wanda ya kasance darektan gudanarwa na NSCIA ya rasu ne a sakamakon wani mummunan hadarin mota da ya yi.

Jaridar The Guardian ta fitar da rahoto cewa Yusuf Chinedozi Nwoha ya gamu da hadari ne a yankin Okene da ke jihar Kogi a kan hanyarsa ta zuwa Owerri. Kawo yanzu ba a samu cikakken labarin abin da ya auku ba,

amma an tabbatar da cewa mutum biyu da hadarin ya rutsa tare da su, duk sun rasa ransu. Wani daga cikin ‘yan majalisar NSCIA, Malam Ishaq Sanni, ya tabbatar da cikawar Yusuf Nwoha a wani bayani da ya fitar na ta’aziyya a ranar Alhamis. Sanni ya ce: “Ina lillah waina ilaehi rojihun. Mun shiga yanayin jimami! Alhaj Yusuf Nwoha, Darektan gudanarwa na majalisar NSCIA ya bar mu yau.”

“Ya rasu a hadarin mota a Okene, a kan hanyarsa ta zuwa Owerri domin ya yi sallar idi. Babu tantama Yusuf ya na cikin mafi alherin cikinmu.” Abokin aikin marigayin ya kara da cewa: “Ya karbi addinin musuluci ne a shekarun 1980s, daga nan ya nemi ilmin addinin musulunci kafi ace kobo.”
“Ya yi karatu a jami’ar Bayero ta Kano. Mun nada shi a matsayin Darektan cibiyar yada addinin musulunci da ke Owerri, wanda Baba Adinnin kasar Yarbawa, Alhaj MKO Abiola, ya asassa.” Marigayin ya kuma yi aiki da hukumar zabe na kasa wata INEC, har ta kai ga ya yi ritaya kwanaki.

“Saboda gaskiya da gogewarsa, an nada shi Darektan harkokin gudanarwa na majalisar NSCIA. Mun yi magana da shi a ranar Litinin inda ya yi mani kukan ulsa, na ba shi shawarar ya nemi magungunan gargajiiya, ban san cewa tattaunawar mu ta karshe ba kenan.” An yi addu’a Ubangiji ya jikan wannan Bawan Allah, ya kuma yi masa rahama.

SOURCE: LEGIT.NG
T
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments