--
'Yan sanda sun kubutar da ma'aikata 600 da aka rufesu tsawon wata 3 a wani kamfanin shinkafa

'Yan sanda sun kubutar da ma'aikata 600 da aka rufesu tsawon wata 3 a wani kamfanin shinkafa



 Rundunar 'yan sanda a jihar Kano ta kubutar da wasu leburori fiye da 600 da aka tursasawa zama a cikin wani kamfanin sarrafa shinkafa mai suna 'popular farm rice' da ke rukunin masana'antu na Challawa a Kano. Ma'aikatan da abin ya shafa sun shaidawa jaridar Premium Times cewa an yi musu barazanar sallama daga aiki ga duk wanda ya yi kokarin barin kamfanin domin zuwa ya gana da iyalinsa.

Jami'an rundunar 'yan sanda sun dira a kamfanin bayan samun sahalewar kotu, sun sallami ma'aikatan tare da kama manajojin kamfanin guda hudu. A cewar ma'aikatan, an hanasu barin harabar kamfanin ne saboda tsoron kar su kwaso cutar korona daga waje idan sun fita. Daya daga cikin ma'aikatan da aka kubutar ya shaidawa manema labarai cewa bai kara fita daga kamfanin ba tun bayan shigarsa a ranar 23 ga watan Maris.

Haruna Salihu, wani ma'aikacin kamfanin ya ce ba bar shi ya fita daga kamfanin ba tun bayan shigowarsa a ranar 28 ga watan Maris. "Iyalanmu sun shiga damuwa, saboda basu ganmu ba, basu san halin da muke ciki ba. Matata da 'ya'yana sun sha zuwa kamfanin domin su ganni, amma ba a taba barina na je bakin kofar shiga kamfani domin ganawa da su ba.

"Dabara suka yi mana; da farko sun bukaci mu zauna na tsawon kwana biyar ba tare da fita daga kamfanin ba, daga baya suka mayar da shi sati biyu, sannan suka mayar da shi wata daya. Yanzu haka mun shafe fiye da wata uku. "Akwai kimanin ma'aikata 600 a kamfanin, ba mu da muhallin kwanciya mai kyau. Ina rokon mahukuntan wannan kamfani su barni na koma gida wurin iyalina," a cewarsa.

Wani daga cikin ma'aikatan ya ce duk da ba a tilasta masa zama a kamfanin ba, an yi masa barazanar cewa za a kore shi idan ya sake ya fita daga harabar kamfanin. Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce sun kama manajojin kamfanin hudu yayin da suka dira kamfanin domin kubutar da leburorin.

"Mun samu ma'aikata da yawa da aka garkame a kamfanin. Kwamishinan 'yan sandan jihar Kano, Habu A Sani, ya bayar da umarnin a gudanar da bincike a kan lamarin. Ya zuwa yanzu mun kama manajojin kamfanin hudu kuma mun fara gudanar da bincike," a cewar Kiyawa.


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "'Yan sanda sun kubutar da ma'aikata 600 da aka rufesu tsawon wata 3 a wani kamfanin shinkafa "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?