LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Saurayi ya kashe budurwarsa ya jefa gawarta rijiya sboda ta ki amincewa da shi lokacin da a ziyarci gidansaROHOTON: LEGIT.NG


Wani saurayi da ake zargi da aikata laifin kisan kai ya bayyana yadda ya kashe budurwarsa, Happiness Winfred, mai shekaru 30, tare da jefa gawarta a rijiya. Saurayin, Shagbada Erigga, ya bayyana hakan ne ranar Talata yayin da aka yi bajakolinsa tare da wasu sauran ma su laifi 32 a hedikwatar rundunar 'yan sanda ta jihar Oyo da ke unguwar Eleyele a garin Ibadan.


Erigga ya ce ya kaiwa Happiness hari ne saboda ta ki amincewa da shi lokacin da ta ziyace shi a gidansa. Ya ce lamarin ya faru ne lokacin da marigayiyar ta ziyarce shi a gidansa da ke yankin Oritoke a unguwar Ojoo a garin Ibadan. "Ta zo gidana da misalin karfe 7:00 na ymmacin ranar Lahadi, na nemeta bayan mun yi wanka amma sai ta ki amincewa, har hakan ta kai ga mun samu sabani.

"Na tambayeta dalilin da yasa sai na roketa koda yaushe kafin ta amince da ni, na mareta, ita ma ta rama. "Ta fadi kasa jini na zuba bayan na nausheta sau uku a makogoro. Na dauki gawarta na jefa a cikin rijiya bayan ta mutu.

"Asirina ya tonu ne bayan daya daga cikin makwabtana ya zo diban ruwa a rijiyar bayan dawowarsa daga aiki.

"Makwabcina ya fahimci ruwan rijiyar ya gurbace, ya sauya kala kuma ya na wari. Daga bisani sun gano cewa akwai gawar mutum a cikin rijiyar. "An kama ni bayan sun kai rahoto ofishin rundunar 'yan sanda," kamar yadda mai laifin ya sanar da manema labarai. Rundunar 'yan sanda ta ce an samu kayan laifi a tare da Erigga da suka hada da wayar salula, agogon hannu, sarka, jakar hannu, takalmi, da sauran wasu kaya mallakar marigayiya Happiness.


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
 LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments