LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Namibia ta fi kowace kasa a nahiyar Afirka tituna masu kyau - Africa Facts Zone kalli ka gani ananROHOTON: LEGIT.NG

Najeriya ba ta samu shiga ba cikin jerin manyan kasashe 13 na Afirka da ke da kyawawan tituna a Afirka yayin da Namibia ta ciri tuta - Seychelles, Eswatini, da Cape Verde sun kasance a mataki na 11, 12 da 13 a jere da juna.

Kasar Afirka ta Kudu tana mataki na shida, yayin da Senegal da Kenya suke kan mataki na bakwai da na takwas a jerin Shafin Africa Facts Zone mai fidda kididdiga kan sha'ani da al'amuran da suka shafi kasashen nahiyyar Afirka, ya bayyana jerin kasashen nahiyar mafiya kyawun tituna.

Kamar yadda Hukumar tattalin arziki ta duniya WEF ta fitar a kididdigar ta 2019, ta bayyana wasu kasashen Afrika 13 masu nagartattun tituna gwanin sha'awa. Africa Facts Zone ta wallafa jerin kasashe 13 mafi kyawaun tituna a nahiyyar Afrika.

Kasar Namibia ta ciri tura, yayin da ta yiwa dukkanin kasashen Afrika zarra da fintikau ta mafi kyawun tituna luwai-luwai gwanin sha'awa. Kasar Masar mai kayatuttun gine-gine ta biyo baya a mataki na biyu cikin jerin kasashin nahiyar Afrika da suka fi kowanne tituna masu kyau.

Sauran kasashen da suka fito a sahu biyar na farko sun hadar da Rwanda, Morocco, da Mauritius. Kasashe irin su Kenya, Senegal, Afrika ta Kudu, Algeria da kuma Tanzania, su ma ba a barsu a baya ba, cikin jerin kasashen da gwamnatocinsu suka inganta musu tituna. Ga jerin kasashen 13 da matakin kowace kasa kamar haka: 1. Namibia 2. Egypt 3. Rwanda 4. Morocco 5. Mauritius 6. South Africa 7. Senegal 8. Kenya 9. Tanzania 10. Algeria 11. Seychelles 12. Eswatini 13. Cape Verde


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments