--
Ku zage damtse, ko mu saita muku hanya - Lawan ga Shugabannin tsaro

Ku zage damtse, ko mu saita muku hanya - Lawan ga Shugabannin tsaro



Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya yi kira ga hafsoshin tsaro da su zage damtse domin gudun saukesu daga mukamansu. A yayin zantawa da manema labarai bayan ganawarsa da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Lahadi, Lawan ya jajanta yadda rashin tsaro ya tsananta a kasar nan, gidan talabijin din Channels ya ruwaito. Ya ce majalisar dattawa na ta kokari tare da assasa samar da kayan da jami'an tsaro ke bukata don samun ingantaccen aiki a kasar nan.

"Kasar nan tana fuskantar mummunan kalubalen tsaro kuma na tattauna da shugaban kasa a kan abinda ya dace mu yi don inganta tsaro a kasar nan," yace. "Kuma mun aminta da abinda majalisar dattawa tace. Ta tabbatar da cewa a shirye take don amincewa da wani sabon kasafin kudi a kan fannin tsaron kasar nan. "Ta hakan ne za mu iya inganta cibiyoyin tsaro don samun karfin yakar Boko Haram a yankin arewa maso gabas da kuma matsalar 'yan bindiga a sauran yankunan arewa.

"Abu na biyu, majalisar dattawa ta aminta da cewa dole ne mu kara yawan jami'an tsaro a cibiyoyin tsaron kasar nan da suka hada da sojin kasa, sama, ruwa, 'yan sanda da sauransu. Muna bukatar karin su," yace. Ya kara da cewa, "sashi na 12, sakin layi na biyu na kundun tsarin mulkin Najeriya ya bayyana cewa amfanin gwamnati shine samar da tsaro tare da walwala ga jama'a "A don haka, bamu da wata walwala idan bamu shawo kan matsalar tsaro da ta addabemu ba.

"Ina tunanin dole mu fada wa kanmu gaskiya, cewa kalubalen tsaro ballantana a arewa na bukatar dagiya. A don haka ne dole shugabannin cibiyoyin tsaro su dage. Dole ne mu tsara yadda za mu shawo kan al'amarin. "Idan bayan mun bada tallafi muka ga wani bai kai yadda muke tsammani ba, dole ne mu saita masa hanya saboda rayukan 'yan Najeriya na da matukar amfani. Amfaninsu ya zarce komai."

 Har ila yau, Ahmad Lawan ya samu tattaunawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan rikicin cikin gida da ya addabi jam'iyyar mai mulki kuma yake barazanar tarwatsa ta.


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Ku zage damtse, ko mu saita muku hanya - Lawan ga Shugabannin tsaro "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?