LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Kotu ta saki matashiyar da ta kashe tsoho da yayi yunkurin yi mata fyade

ROHOTON: LEGIT.NG

Kotun majistare da ke jihar Legas ta saki wata matashiyar budurwa mai shekaru 15 sakamakon kashe wani tsoho mai shekaru 51 - Ta kashe tsohon mai suna Babatunde Ishola bayan ya yi kokarin yi mata fyade

Mai shari'a Philip Adebowale Ojo ya soke zargin da ake yi wa matashiyar da ke aji shida na sakandare bayan shawarar da ya samu daga hukumar gurfanarwa ta jihar Legas Wata kotun majistare da ke jihar Legas ta saki wata matashiyar budurwa mai shekaru 15 da ta kashe wani tsoho mai shekaru 51 mai suna Babatunde Ishola. Matashiyar budurwar ta tabbatar da cewa kare kanta ta yi yunkurin yi bayan tsohon ya yi yunkurin yi mata fyade.

Mai shari'a Philip Adebowale Ojo ya soke zargin da ake yi wa matashiyar da ke aji shida na sakandare bayan shawarar da ya samu daga hukumar gurfanarwa ta jihar Legas. Daraktan ofishin kare kai na jihar Legas, Dr. Babajide Martins, wanda ofishinsa ya kare matashiyar ya nuna gamsuwarsa a kan hukuncin kotun.

A wani labarin kuma, mun ji cewa wani matashi mai shekaru 26 ya tsallaka rijiya da baya a cikin kwanakin karshen mako bayan da ya lalata yarinya mai shekaru bakwai. Fusatattun mazauna kauyen Akparoji da ke yankin Owukpa na karamar hukumar Ogabdigbo na jihar Benue ne suka yi yunkurin banka masa wuta. Jaridar Daily Trust ta gano cewa, an kama mutumin mai suna Patrick Onoja Igah yana lalata da yarinya mai shekaru bakwai a farfajiyar coci.

Mazauna yankin sun ce, Ogah wanda aka fi sani da Omolomo, dan asalin Ogwurute Itabono ne a Owukpa. An yi mishi dukan kawo wuka har an kusan kashe shi kafin 'yan banga su kwace shi tare da mika shi hannun 'yan sanda. Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Benue, DSP Catherine Anene, ya tabbatar da aukuwar lamarin ga Daily Trust ta wayar tarho. Ya ce a halin yanzu wanda ake zargin yana hannun 'yan sanda.

"Zan iya bada tabbacin cewa matashi mai shekaru 26 da aka kama da laifin yi wa yarinya mai shekaru 7 fyade yana hannun mu," Anene yace. A cikin kwanakin nan ne jama'a a fadin duniya ke ta cece-kuce a kan yawaitar cin zarafin kananan yara da yi wa 'yan mata fyade da ya yawaita.


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments