--
Kiwon lafiya: Kukaranta Alamomi 7 da zaku gane koda ta fara samun matsala

Kiwon lafiya: Kukaranta Alamomi 7 da zaku gane koda ta fara samun matsala



Masana harkar lafiya sun bayyana cewar koshin lafiyar koda na daga cikin sirrukan dadewa a duniya ba tare da gajiyawar jiki ba,

Koda na taka muhimmiyar rawa wajen tace wa da cire sinadarai ma su guba daga abubuwan da mutum ya sha. Koda na da alaka da sarrafa yanayin jinin jikin ta mutum,

Bisa la'akari da muhimmanci koda a jikin mutum ne yasa muka bunciko muku wasu daga cikin alamomi 7 da ke nuna cewar koda ta samu matsala, kamar yadda masana su ka tabbatar.

1. Kumburi da taruwar ruwa a sassan jiki: Daya daga cikin alamomi na sahun farko da ke nuna cewar koda ta fara samun matsala akwai taruwar ruwa a cikin jiki da kale haifar da kumburi. Sassan jiki da wannan matsala ta fi bayyana su ne; sahun kafa, hannaye, kafafu, ciki, da fuska.

2. Sukurkucewar mafitsara: Yayin da mutun ya fuskanci ba ya iya rike fitsari kamar yadda ya saba a baya, ya gaggauta zuwa asibiti domin gudanar da bincike a kan yanayin aikin kodar sa.

3. Gagarumin canji a launin fitsari: Launi, kala, da zarnin fitsari na daga cikin abubuwan da ake amfani da su wajen fahimtar aikin koda.

Idan fitsari yana kumfa ko tsananin zarni ko wari ko mutum ya ke jin zafi yayin fitar fitsari ko ganin jini a fitsari alamu ne da ke nuni cewar aikin koda ba ya tafiya yadda ya kamata.
4. Kuraje a fata: Duk da akwai abubuwa da yawa da kan iya haddasa fitowar kuraje a jikin mutum, gazawar koda wajen tace wasu sinadarai ma su guba kan iya haddasa fesowar kuraje a jiki.

5. Ciwo a kashin baya (kugu): Matsalar koda na jawo yawaitar samun ciwon baya, musamman a kugu.

6. Hawan jini: Masana lafiya sun bawa ma su matsalar koda shawarar su ke yawan ziyarar asibiti domin duba yanayin jininsu, saboda koda na taka rawa wajen daidaita sinadaran fatashiyom da sodiyom, sindaran da ke da alhakin da alhakin daidaita yanayin jini a jiki.

7. Yawan gajiya da kasala: Yayin da koda ta fara samun matsala, mutum kan tsinci kansa cikin yawan samun kasalar jiki da gajiya, wasu lokutan mutum har jiri ya kan ji da rashin samun natsuwa.



KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Kiwon lafiya: Kukaranta Alamomi 7 da zaku gane koda ta fara samun matsala "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?