LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

An cafke matashi da yake kokarin sace yaro dan shekara 2 a KanoA jiya Asabar ne aka kama wani matashi mai shekaru 20 a duniya, a lokacin da yake kokarin yin garkuwa da wani yaro mai shekara biyu a duniya akan titin Aba, dake Sabon Gari cikin birnin Kano.

An ruwaito cewa ‘yan sanda ne suka ceto rayuwar saurayin daga hannun matasa wadanda suka kama shi a lokacin da yake shirin sace yaron.

Saurayin wanda aka boye sunanshi, ya shiga wani gida mai bene hawa daya, inda ya dauko yaron, amma asirin shi ya tono a lokacin da yake hanyar fitowa daga gidan, inda wani makwabcin gidan ya ganshi da yaron.

Cikin gaggawa ya sanar da jama’a, inda aka kama matashin ake shirin sanya masa wuta. An samu jikin shi cike da guraye da layu, wadanda yake tunanin zasu taimaka masa a hali irin wannan, sai dai a wannan karon sun bashi kunya.

Daga baya jami’an tsaro sun isa wajen suka karbe matashin suka tafi dashi ofishinsu dake Nomandland domin cigaba da bincike a kanshi.

Sai dai har ya zuwa yanzu dai ba aji ta bakin jami’in hulda da jama’a na hukumar ‘yan sandan jihar, DSP Abdullahi Haruna, game da lamarin.KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments