LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Yawan ‘yan Najeriya da suke jira su saci kudin Najeriya sun fi yawan wadanda suke sata yanzu – Dino Melaye

Tsohon sanata mai wakiltar jihar Kogi ta yamma, Sanata Dino Melaye ya wallafa wani rubutu a shafinsa na Instagram, inda ya bayyana halin da Najeriya take ciki.

Dino ya bayyana cewa Najeriya na cikin wani hali, saboda akwai mutane masu yawan gaske da suke jira su samu damar da za su saci kudin al’umma.

Ya ce: “A Najeriya yawan mutanen da suke jira su samu damar da za su saci kudin na Najeriya na al’umma yafi yawan mutanen da suke cikin gwamnati a yanzu suke satar kudaden jama’a. Muna cikin tashin hankali.”
A makon da ya gabata Mun kawo muku rahoton yadda aka sha tataburza da tsohon sanatan, bayan an bukaci ya sayar da kadarorinsa ya taimakawa al’ummar yankinsa da kudin.

Dino ya bayyana cewa kudin da yake dashi ba zai iya ciro ‘yan Najeriya daga halin da suke ciki ba, inda ya ce matukar ya sayar da kadarorinsa to talaucewa zai yi.

A karshe ma dai sanatan ya bayyana cewa yana addu’a Allah ya kara masa arzukin da zai kara siyan kadarori, saboda su yafi so a rayuwar shi.


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments