LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Yanzu-yanzu: Sabbin Mutane 146 sun kamu da Coronavirus, Legas da Kano a gabaHukumar yaki da cututtuka masu yaduwa a kasa (NCDC) ta ce annobar cutar covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 146 a fadin Najeriya. Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da NCDC ta fitar da misalin karfe 11:55 na yammacin ranar Talata, 12 ga watan Mayu, 2020.

A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na tuwita, ta sanar da cewa karin sabbin mutane 146 din sun fito daga jihohin Najeriya kamar haka;

57-Lagos, 27-Kano, 10-Kwara, 9-Edo, 8-Bauchi, 7-Yobe, 4-Kebbi, 4-Oyo, 3-Katsina, 3-Niger, 2-Plateau, 2-Borno, 2-Sokoto, 2-Benue, 1-Gombe, 1-Enugu, 1-Ebonyi, 1-Ogun, 1-FCT, 1-Rivers

A yau, an sallami mutane 57 bayan sun samu waraka kuma an yi rashin mutane 8. NCDC ta ce ya zuwa karfe 11:55 na yammacin ranar Talata, 12 ga watan Mayu, akwai jimillar mutane 4787 da aka tabbatar da cewa suna dauke da kwayar cutar covid-19 a fadin Najeriya.

An sallami mutane 959 bayan an tabbatar da sun warke sarai, a yayin da cutar ta hallaka jimillar mutane 158. l

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments