LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Masana sun nuna damuwa a kan raguwar adadin ma su kamuwa da korona a KanoROHOTON: LEGIT.NG

Darektan cibiyar binciken cututtuka ma su yaduwa (CIDR) a jami'ar Bayero da ke Kano (BUK), Farfesa Isa Abubakar, ya ce raguwar adadin ma su kamuwa da cutar korona a jihar abin damuwa ne. Ya ce raguwar alkaluman ma su cutar a Kano ba ya nufin cewa jama'a ba sa kamuwa da cutar a zahiri. Farfesan ya yi gargadin cewa raguwar alkaluman ma su kamuwa da korona a Kano ba alama ce da ke nuna cewa an fara samun saukin annobar a jihar ba.

 Kwararren ya bayyana hakan ne yayin da ya ke gabatar da jawabi bayan gidajen sayen da man fetur na A. A. Rano da Aliko Oli sun bawa cibiyar CIDR gudunmawar na'urar gwajin cutar korona. Ya yi zargin cewa gwamnatin jihar Kano ba ta bayar da adadin samfurin jinin jama'ar da ya kamata a yi wa gwajin cutar korona.

A cewar Abubakar, raguwar adadin ma su kamuwa da na ma su dauke da kwayar cutar a jihar Kano ba alama ce ta cewa an fara samun lafawar annobar a jihar ba.

"A matsayina na kwararre, zan yi matukar farin cikin ganin an fara samun raguwar adadin ma su cutar korona a Kano, amma har yanzu lokacin da za a fara samun raguwar adadin ma su dauke da cutar ba i yi ba, a saboda haka bai kamata mu fara murna ba," a cewarsa.

Sai dai, jagora a kwamitin yaki da annobar cutar korona a jihar Kano, Dakta Tijjani Hussaini, ya musanta cewa gwamnati ta na kwangen aika adadin samfur din da ya kamata a yi wa gwaji zuwa cibiyar gwaji ba. Ya bayyana cewa daga ranar 24 zuwa 30 ga watan Mayu,

an aika samfur 1,018 domin gudanar da gwaji amma 70 ne kawai aka samu su na dauke da kwayar cutar. "A yanzu haka maganar da na ke yi, mun aika samfur zuwa cibiyoyin gwaji da ke BUK, asibitin kwararru na Muhammadu Buhari, da asibitin Malam Aminu Kano.

Mun aika samfur 1,018 a cikin sati guda, wanda daga ciki aka samu 70 da ke dauke da kwayar cutar korona," a cewarsa. Jagoran ya bayyana cewa karin cibiyoyin gwaji da aka samu a jihar Kano ya kawo raguwar adadin kwanakin da ake dauka kafin sakamakon gwaji ya fito.


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments