LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Hotuna: Mayakan Boko Haram na ci gaba da mika wuya ga sojin NajeriyaROHOTON: LEGIT.NG

A yayin da dakarun sojin Najeriya ke gab da samun nasarar karar da ‘yan Boko Haram a yankin arewa maso gabas, mayakan na gaggawar mika kansu ko kuma a damko su tare da makamansu. A yayin da hakan ke faruwa, jami’an rundunar sojin Najeriya na ci gaba da kai musu hari tare da kone musu makamai da maboyarsu.

A ranar 29 ga watan Mayun 2020, mayakin Boko Haram, Muhammad Abubakar wanda aka fi sani da Babagana ya mika kansa ga bataliya ta 242 da ke Monguno a jihar Borno. Kamar yadda binciken farko ya bayyana, matashin mai shekaru 19 ya shiga kungiyar ne a shekara daya da ta gabata a Shaharam, kuma ya taka rawar gani a harin da aka kai Tumbun Saje.

A yayin nuna dana-sanin miyagun ayyukansa, Babagana ya yi kira ga sauran abokan ta’addancinsa da su mika kansu ga dakarun sojin Najeriya kafin lokaci ya kure musu. A ranar 24 ga watan Mayun 2020, Malam Adamu Yahaya wanda aka fi sani da Saad Karami ya mika kansa ga bataliya ta 242 ta Monguno.

A wani ci gaba na daban, Muhammad Kabudumi wanda aka fi sani da Amir Sabat ya mika kansa ga bataliya ta 242 da ke Monguno. Kabudumi ya amsa cewa ya shiga kungiyar amma ya musanta shiga ayyukan kungiyar kwata-kwata. Amma kuma yace yana aikace-aikace a sansanin ‘yan ta’addan da ke Abadam, Malam Fatori da Duguri karkashin shugabancin Muhammadu Lawan, babban kwamandansu.

A ranar 28 ga watan Mayun 2020, dakarun sojin Najeriya da ke sansani na 11 a Gamboru, karamar hukumar Ngala a jihar Borno, sun kai samame kauyukan Gulwa, Diime, Musiri, Wuri Bari, Mada, Sangaya, Jarawa, Mutu, Isari da Mudu. Dakarun su bincike kauyukan amma basu samu kowa ba sai makaman ‘yan ta’addan da suka tsere suka bari.

Sun samu bindiga kirar AK 47 guda 2, bindigogin toka 20, wasu bindigogi 4, kwari da baka daya da kuma tutocin mayakan 15. Hakazalika, dakarun sun ceto mata hudu dattawa da mayakan suka yi garkuwa da su. najeriya


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments